YAN TA ADDA SUN KASHE SOJA 15 SUN JIKKATA 18 A KATSINA

0

YAN TA ADDA SUN KASHE SOJA 15 SUN JIKKATA 18 A KATSINA
@ jaridar taskar labarai
Wani kwantar bauna da yan ta adda sukayi wa sojan Najeriya a dajin shimfida dake karamar hukumar jibia ta jahar katsina yayi sanadin mutuwar sojan Najeriya 15 an kuma jikkata guda 18 kamar yadda wata majiya ta tabbatar wa wannan jaridar a yau lahadi.
Kwantar baunar da ta adin ya faru ne, a jiya asabar a dajin shimfida yankin tsamben tsauni da ke kilomita kasa da Goma da garin jibia.
An tabbatar wa da jaridar nan cewa, sojan sun dawo daga wani aiki ne. Akan fulani masu dauke da miyagun makamai a dajin.sojan su kuma yi nasara akan fulanin suna kan hanyarsu ta dawowa cikin farin cikin nasara , sai akayi masu wannan kwantar bauna.
Sojan sunyi nasarar tsare kansu, har suka kori yan ta addar kuma suka Nemi dauki aka zo aka tafi da gawarwakin wadanda aka jikkata da wadanda suka rasa ransu kamar yadda majiyarmu ta tabbatar mana.
An ce soja sun sake shiri inda suka sake fafarar yan yan ta addar har cikin daji.suka kashe da yawa daga cikin su.duk sojojin da lamarin ya rutsa da su.an kaisu asibitin gwamnatin tarayya ta katsina.
Wani bafullace da ya tsira a yankin yace yaga sama da babura dari ya she a inda ake jin anyi fafatawar.sannan ga gawarwaki nan fululu.
Dajin shimfida dake karamar hukumar jibia.yana hannun mayaka dake karkashin wani da ake Kira dangote ne. Wanda ba Wanda ya San kamanninsa sai lokacin da aka fara tattaunawar sasanci a katsina.ya amince aka dau hotunsa rike da AK47.hoton da jaridar The links ta samu.
An sha yin sasanci da mutanensa.ya kuma koma ruwa.
Munyi kokarin jin ta bakin hedkwatar tsaro ta Najeriya, amma abin yaci tura,mun aika da sakon rubutu na waya. Har zuwa rahoton nan babu
amsa
________________________________________________
Jaridar taskar labarai, jarida ce dake bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma yar uwarta turanci dake a www.thelinksnews.com. da sauran shafukan sada zumunta. duk sako a aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here