AN KORI SHUGABAN JAM’IYYAR APC NA KANKIYA DAGA JAM’IYYAR

0

AN KORI SHUGABAN JAM’IYYAR APC NA KANKIYA DAGA JAM’IYYAR
~~~ Ban san da wannan magan ba… Danjuma Rimaye
@ taskar labarai
Kwana guda da kammala taron shuwagabannin jam’iyyar APC a jihar Katsina, sai wani bangare kuma ya yage, wanda hakan ke nuni da irin kalubalen da jam’iyyar take ciki.

A wani taron manema labarai da wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ta APC suka kira a jiya Litinin sun koka ne kan yadda uwar jam’iyyar ta jiha take watsi ko kuma rikon sakainar kashi ga jam’iyyar, daya daga cikin masu ruwa da tsakin Ali Jimi ya bayyana cewa, tun a watan Afrilun da ya gabata shugabannin jam’iyyar a matakin karamar hukuma suka yi taro suka tsige Danjuma Rimaye shugaban Jam’iyyar daga jagorancin da yake, kuma suka vada takarda ga jam’iyya a rubuce har ka nada kwamiti karkashin jagorancin mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Daura Usman Osi, wanda kwamitin sa ke aiki, amma kwatsam sai suka ga wata takarda na yawo a ranar juma’ar da ta gabata wai an mayar da shi bisa kujerarsa, wanda wannan sam saba ka’ida ne da keta mutuncin jam’iyya.

Wannan yasa shugabanini jam’iyyar na mazabar shi wanda aka mayar din suka yi taro suka kada kuri’ar korar shi daga jam’iyyar kwatakwata, sakamakon zagon kasa da bita da kulli da suke zargin ahi da yi wa jam’iyyar.

Wata majiya kuma ta sheda wa wanann jaridar cewa a taron da aka yi na shugabannin jam’iyyar APC a ranar Asabar anga shi shugaban jam’iyyar a wajen tare da wani da ba a tantance ba yana amnatasa a matsayin sakataren jam’iyya na karamar hukumar Kankiya duk da cewa, shi sakataren bai halarci wajen ba.

Wata majiya ta shedawa Jaridar Taskar Labarai cewa uwar jam’iyya ta aika takardar sammace ga sauran shugabanin da suka kauracewa taron da aka gudanar a ranar asabar domin a tuhume su kan dalilin rashin zuwansu a yau Talata.

See also  Shugaban masu buƙata na ƙasa yace tabbas Sen, Atiku Bagudu jagorane kuma abun koyi.

Jaridar Taskar Labarai ta tuntubi Danjuma Rimaya wanda shi ne ake wannan badakalar akan sa inda ya bayyana cewa, shi bai san da wannan maganar ba, domin ko kwanakin baya sun taba cire shi amma, aka yi bincike sai ba a same shi da laifi ba, kuma akan wannan rigimar Ma’ajin jam’iyya na kasa da wasu sun zauna da gwamna domin warware rikijin ya bayyana cewa, duka rigikar kan jagorori biyu ne ake yinta wato Acr. Ahmad Musa Dangiwa da Sanata Ahmad Babba Kaita.
Shugaban jam’iyyar kuma ya zargi cewa Danmajalissar Jiha ne ya tara wadannan mutane ya bukaci da su tsige shi.

A ta bangaren Danmajalisar jiha mai wakiltar Kankiya kuwa Hon. Salisu Hamza Rimaye da Taskar Labarai ta tuntube shi ya bayyana cewa wannan magana ta Danjuma Rimaye Tatsuniya ce kawai, domin ko kwanakin baya da suka kore shi bai ma san an yi ba, balle kuma yanzu da suka kore shi daga jam’iyya, kuma shi a iyar saninsa bai san akwai wata rigima tsakanin Acr. Ahmad Musa Dangiwa da Babba Kaita ba. Wannan abu da ya faru kuma shi ma an bashi takarda ne a rubuce, yana jawo hankalin shi Tsohon shugaban jam’iyya da ya daina ayyana shi a cikin rikice-rikicensu, domin shi bai da masaniya.

Jam’iyyar APC dai na fama sa rikicin cikin gida a jihar Katsina, ko satin da ya wuce irin haka ta faru da jam’iyyar a karamar hukumar Mashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here