DA YIWUWAR SAMUN AMBALIYAR RUWAN SAMA A JIHAR KANO

0

DA YIWUWAR SAMUN AMBALIYAR RUWAN SAMA A JIHAR KANO- Rahoto

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Hukumar nan da ke kula da yanayi ta ƙasa da ta kula da ayyukan bayar da agajin gaggawa suna fadakar da al’umar kasar nan game da matakan kaucewa ambaliyar ruwa.

Ita ma hukumar kula da kogunan Hadejia da Jama’are ta ce ta yi tsare tsaren kubutar da gonakin manoma daga wannan annoba a yankunan jihohin Kano, Jigawa da kuma Bauchi.
rahoto da hukumar kula da yanayi ta ƙasa ta fitar a makon jiya, ya yi hasashen cewa, jumlar kananan hukumomi 102 ne daga cikin 774 na kasar nan, ka iya fuskantar ambaliyar ruwa a damunar bana.

Rahoton hukumar ya nuna a jihar Kano, kananan hukumomi 17 ne cikin 44 na jihar zasu iya fuskantar ambaliyar.

Wasu daga cikin kananan hukumomin sun hada Kura, Warawa, Rimin Gado, Gwarzo, Kumbotso da Nasarawa.

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce rahotan na hukumar kula da yanayi ta ƙasa ya zaburar da su wajen daukar matakan da suka dace.

Bayan faduwar Damina dai daruruwan mutane sun yi asarar muhallai da dama a Kano, haka kuma ana samun ambaliyar ruwa da ke lalata amfanin gona na miliyoyin nairo a kowace shekara, al’amarin dake jefa manoma halin ni ya su.

To amma hukumar kula da kogunan Hadejia da Jama’are mai hurumi a sassan jihohin Kano Jigawa da kuma Bauchi, ta ce ta dauki matakan da suka kamata domin kubutar da manoman dake karkashin kulawar ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here