JANAR BURTAI ZAI MAKA MAHADI KOTU

0

JANAR BURTAI ZAI MAKA MAHADI KOTU
@ Taskar labarai
Lauyan janar Burtai babban hafsan sojan Najeriya ya bayyanawa manema labarai cewa sun ba mahadi shehu awa arba in da takwas ya janye zargin da yayiwa Burtai kuma ya buga janyewar da ban hakuri a jaridu guda uku cikin awa 48 ko kuma su kai shi kotu,su bukaci hukunci da diyyar naira bilyan Goma.!!
Lauyan Burtai ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gabatar a yau a dakin taro na sakatariyar yan jarida dake katsina.
lauyan yace zargin da mahadi shehu yayi ma Wanda yake karewa ya bata masa suna kuma ya bakanta shi a gaban jama a.da mutanen katsina dake kallon shi da mutunci.
Lauyan yace zargin na mahadi shehu, tuni gwamnatin katsina ta karyata.ga takardar.inda ya daga ta sama kowa ya ganta. don haka mahadi shehu ya tabbatar da zarginshi ko su tafi kotu.
Kwanan nan wani Dan kasuwa mazaunin Kaduna,,dan asalin katsina. Mai suna mahadi shehu yana fitar da wasu zarge zarge akan gwamnatin katsina.
Zargin da hukumomin tsaro daban daban na ta bincike akai.kamar hukumar EFCC da ICPC da rundunar yan sanda.da bangaren sashen sirri na rundunar soja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here