NIGERIYA KASAR MU TA GADO

0

NIGERIYA KASAR MU TA GADO……

Daga Nasir Salisu Zango

Shugaban Hukumar bunkasa yankin Niger Delta ya tayar da aljanu a gaban kwamitin majalisar wakilai dake bibiyar almundahana a hukumar, shi kuma ministan ma’aikatar Godswill Akpabio yace kaso 60 cikin 100 na kwangilolin da aka bayar a ma’aikatar mambobin majalisar aka baiwa.

Kuma an tashi daga taron Ana gaggaisawa, karshe kuma shikenan an rufe wannan shafin Sai kuma na gaba.

Wannan fa duk suna faruwa ne zamanin Baba me gaskiya zamanin da ake bankado almundahana idan an gama bankadowa Sai a bar maganar a saka ta a Mala, watakila Dai ko baba Allah ya Isa yake musu domin abin nasu yayi yawa, Nima Ina ga kawai Hakan za a yi a ringa yi musu Allah ya Isa kawai domin kudin da ake magana sun wuce malala gashin tinkiya, su kuma yan majalisa da aka ce ku ake baiwa wannan kwangila me maiko Yaya za’ayi Kenan allura zata tono garma.

See also  Rwanda ta ɗaure mai sukar gwamnati a shafin YouTube.

Allah ya kawo wa talakan Lanjeria mafita ta gaske ba ta Kiran lamba ba. Fakat.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here