GWAMNATIN KANO TA DAKATAR DA BUKUKUWAN BABBAR SALLAH
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da dakatar da dukkanin wasu bukukuwan da za’a gudanar a lokacin babbar sallah dake gabatowa saboda dakile yaduwar cutar Corona.
Jawabin haka ya fito ne daga Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Muhammad Garba ga manema kabarai a yau, inda yace za’a gabatar da idi babbar sallar ne bisa kiyaye dokokin masana a fannin lafiya akan cutar Corona.
Muhammad Garba ya kara da cewa sarakunan Gaya da Karaye da Kuma Bichi zasu gabatar da sallar ne a masarautunsu.