HARSHEN HAUSA YA CIRI TUTA

0

HARSHEN HAUSA YA CIRI TUTA

Shugaban manyan masallatan nan biyu (Ka’abah da Madinah), Sheikh Abdur-Rahman Bin Abdul-Aziyz As-Sudais, ya bada umarnin a fassara Hudubar ranar Arafah na wannan shekarar kai tsaye cikin manyan Harsunan duniya guda goma, ciki har da harshen Hausa, hukumomin masallatan sun duba cewa akwai mutane sama da miliyan dari da saba’in dake jin harshen Hausa a duniya.
.
Yarukan da za’a fassara Hudubar sune:

1. English.
2. Malay.
3. Urdu.
4. Persian.
5. French.
6. Chinese.
7. Turkish.
8. Russian.
9. Hausa.
10. Bengali.
.
Acikin yarukan guda goma harshen Hausa ne kawai aka zaba daga Africa, wanda yake yaren Africa ne, duba da yanda yaren yake kara yawa a sassan duniya, kuma yake da manyan gidajen TV da Radio a manyan kasashen duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here