HATTARA DAI HUKUMAR KAROTA TA JIHAR KANO

0

HATTARA DAI HUKUMAR KAROTA TA JIHAR KANO

A satin jiya yan kasuwa masu rumfunan temporary a titin Murtala Muhammad suka tsinci talatarsu a laraba bayan da hukumar KAROTA tabi dare ta rushe musu rumfuna ta kuma kwashe musu kaya.

Sai gashi yau yan kasuwar Singa Ado Bayero Rd sun wayi gari da samu nasu notice din daga waccan hukuma na su tattara kayansu nan da wani lokaci suma su tashi.
To ba muna goyon bayan rashin bin doka bane ko karyata, amma a gari irin kano wanda tunkahonsa shi ne kasuwanci, kuma muke rajin wayewa da sanin ya kamata, to ya kamata a ringa bin abubuwa bisa tsari da kallon abinda zai kai ya komo.

Da farko wai ina gwamnati take, ta bar mutanennan suke zaune a wurin nan sama da shekara 30 ba kan ka’idaba ?
Shin gwamnati ta basu wani guri da za su koma?
Tunda an ce ba bisa doka suke zaune ba, menene matsayin harajin da suke biyan gwamnati duk shekara?
Dama gwamnati tana karbar harajin haramtattun gurare?
Abin tsoron a irin wadannan matakan da ake dauka shi ne, kullum gwamnatoci suna rajin yaki da rashin aikin yi da zaman banza, tare da zaburar da al’uma akan neman nakai, sai gashi a gefe guda wata hukuma tana kokarin jefa dubban mutane cikin kakanikayi.

Shawara ga gwamnati
A taimaka a samawa irin wadannan mutane wuraren da zasu koma kafin a tashesu, kuma a nuna musu.
Ina jin tsoran bayan wani lokaci gwamnati ta dawo ta yanka guraren nan ta sayar dasu ga wasu. Hakan zai zubar da kimar gwamnati ya kuma dusashe kwarjinin gwamnati a idon al’umma.

A ringa lura da dama da muke yi da rashin tsaro da aikata laifuka, wanda irin wannan abun yana daya daga cikin sababan hakan.
Duk rumfa daya akalla iyali daya ce, to ka auna ka gani iyali nawa ka tagayyara?
Wadancan na farkon fa suna can suna gararamba, da yawa sun sallami yaransu, ina wadannan yaran suke yanzu? To gashi zaka sake tarwatsa wasu nan da sati daya, anya kuwa hankalin manya ya kawo wannan?

Daga Mal. Aliyu Tamasi, Darakta Consultancy service Aminu Kano College of Islamic and Legal studies Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here