Makarantar Allon Da Ta Shekara 216 Da Kirkira Kuma Har Yanzu Ana Karatu A Jihar Katsina
…a nan tsohon Sarkin Katsina, Kabiru Usman da wasu manya a Katsina suka yi karatun allo
Daga Muhammad Mas’ud Abu
Kamar yadda kuke gani axnan wata makaranta ce dake a wata Unguwa mai suna Tsohuwar Kasuwa cikin birnin Katsina mai cike da tarihi shekaru.
Shehin Malamin da ya gaji makarantar, Malam Mas’ud Muhammad ya shaidawa RARIYA cewa ya ji daga bakin wani kakan sa marigayi Alhaji Usman Koguna cewa wannan makaranta tun 1804 take a hannun Sheikh Malam Abdulmalik shi kuma dan Malan Ladan ne, bayan ya rasu ta koma hannun dansa Malam Jafar. Shi ma bayan Allah ya yi masa cikawa sai ta koma hannun dansa Malam Abdullahi wanda ake cewa Malan Baro.
Ana cikin haka sai Allah ya yi masa rasuwa sai makarantar ta koma hannun dansa Malam Muhammad Mamman wanda shine mahaifin Malan Masa’udu. Bayan ya rasu a 1977 a lokacin Malam mas’ud yana makarantar boko a matakin sakandire sai wani kanen kakansa wanda ake wa lakabi da Malam Minsharaba ya cigaba da rike makarantar tare da Malam Masa’ud. Kasancewa ya tsufa Malam Masa’ud kusan shine karfin makarantar, ana haka har Allah ya yi masa rasuwa sai Malam Mas’ud ya cigaba da tafiyar da makarantar har zuwa yanzu tare da taimakawar wasu daliban makarantar irin su Ali wanda a yanzu shine liman na Burged na soja dake Keffi. Sai Aminu wanda a kewa lakabi da Dan Dila, Yazid, Malam Mansir da sauransu.
Malam Mas’ud ya kara da cewa a yanzu makarantar ta kai shekara Arbain da uku a hannunsa, kuma akwai manyan mutane wadanda suka yi wannan makaranta irinsu marigayi Sarkin Katsina Kabir Usman, mataimakin gwamna Alhaji Mannir Yakubu, Farfesa Sama’ila Junaid da daibsauransu.
Malam ya kara da cewa akwai mutanen da aka yaye wadanda a yanzu wasu sun bude makarantar su wasu na Maiduguri, wasu ba ma a nan kasar ba har da waje.
Ya kara shaida mana cewa ya samu kalubale da yawa amma da ya yi hakuri a yanzu komai ya wuce, inda a yanzu shi da iyalin sa ne ke kula da makarantar sai kuma wasu daga cikin daliban makarantar.