TARIHI MARAS DADI: ASHE DALLAZAWA SUN SHA AZABA?

0

TARIHI MARAS DADI: ASHE DALLAZAWA SUN SHA AZABA?

Daga Jaridar Taskar Labarai

Wata mujalla da yanzu ta karade yanar gizo, mai suna Katsina City News, wadda kamfanin Matasa Media Links Katsina suka fara bugawa ta fito da wani rubutu wanda ya nuna irin ukuba da azaba wadda gidan sarautar Dallazawa suka sha bayan sun bar mulki.

Rubutun wanda ya fito a shafin mujallar na 11 zuwa 14 da taken zuriyar Dallazawa a Katsina. Ya bada bayanin tarihin asalin su waye Dallazawa, da yadda suka yi mulki da yadda zuwa Turawa suka sa sarkin Katsina Abubakar na lokacin ya na da Durbi Muhammadu Dikko ya zama shi ne wakilin masarauta ga Turawa.

Labarin mai ban tausayi ya nuna yadda aka yi wa sarkin Katsina Abubakar sharri aka raba shi da sarautar, aka ba sarki Yaro shi ma cikin Dallazawa. Shi ma aka yi masa sharri,
aka ba sarkin Katsina Muhammadu Dikko, daga nan suka fara shiga kuncin rayuwa.

See also  Dillalan Naman Jaki Na Neman Diyyar Biliyan Daya Daga Hukumar Kwastam

Rubutun ya nuna yadda aka fara killace Dallazawa kamar wasu bayi a Kaita, cikin talauci da kuncin rayuwa.
Sai da Turawa suka matsa ma sarki Dikko ya basu kasa, sai ya basu dajin Tsaskiya ba ruwa ba kasar noma ga dajin rugu.

Wannan ne sanadin fashewar Dallazawa suka fantsama duniya, rubutun ya nuna sai daga baya dayllazawa suka dawo Safana.

Rubutu ne, da aka rika yi da kawo hujja daga kundaye da littattafan tarihi.

Mujallar da aka fara sakin ta a yanar gizo, bugaggarta zata fito a ranar Talata mai zuwa, kuma kyauta ce ga wanda yayi sa’ar samun kwafi, dole in ka karanta rubutun Dallazawa sai kayi kwalla.
_______________________________________________
Taskar labarai na a www.taskarlabarai.com da ‘yar uwarta Turanci a www.thelinksnews.com duk sako ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here