Dauda Lawal Ya Yi Bayanai Kan Magu A Gaban Kwamitin Binciken Shugaba

0

Dauda Lawal Ya Yi Bayanai Kan Magu A Gaban Kwamitin Binciken Shugaban Kasa

Tsohon Babban Daraktan Bankin ‘First Bank Nigeria Plc’, Dauda Lawal ya bayar da shaidar tonon silili ga tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu a gaban kwamitin Shugaban Kasa wanda Mai Shari’ah Salami ke jagoranta.
Majiyarmu da ke da kusanci da kwamitin ta tabbatar da cewa, Kwamitin Bincike na Shugaban Kasa ya gayyaci Dauda Lawal ne a ranar Asabar din da ta gabata, 25 ga watan Yulin shekarar 2020 a matsayin shaida ga binciken da ake gudanarwa kan Magu.
Sai dai a daidai lokacin da Dauda Lawal ke tsaka da bayar da bahasi kamar yadda kwamitin ya bukata, kwatsam! Sai ga tsohon Shugaban na EFCC, Ibrahim Magu ya shigo. Wanda kuma a tsari bai kamata ya zo wurin ba, sai karfe 3:00 na rana. Da farko membobin kwamitin sun nemi su hana Magu zama wurin, wanda bayan ya roki a barsa ya saurari bahasin Dauda din, sai suka bar shi.
Kwamitin Binciken ya gayyaci Dauda ne domin ya yi musu karin haske kan zargin da ya yi wa EFCC a kwanakin baya, wanda ya rubuta a rubuce ya aike wa ofishin Ministan Shari’a.
Dauda Lawal ya maimaitawa kwamitin binciken irin bayanin da ya gabatar a gaban mai Shari’a Muslim Hassan na Babbar Kotun Tarayya dake Legas a shekarar 2017. Inda a cikin bayanin nasa ya ja da matakin da EFCC ta dauka na daskarar da asusun ajiyansa na banki tare da kwashe mishi kudi.
Haka kuma Dauda Lawal ya bayyana yadda EFCC din karkashin tsohon Shugabanta, Ibrahim Magu ta tsare shi na tsawon kwanaki 11 a shekarar 2016, tare da yi mishi barazanar cewa za su sake shi ne kawai idan ya dawo da wasu kudade.
Dangane da yadda ya amshi Dalar Amurka miliyan 25 kuwa, Dauda Lawal ya ce wani abokinsa mai suna Stanley Lawson ne ya roke shi da ya amshi kudin a watan Maris din 2015, kuma ya bayar da asusun bankin da ya ke so ya zuba mishi kudin.
Dauda ya ce: “Ni ban san daga ina aka samo kudaden ba. Sannan kuma na bi dukkanin ka’idoji da dokokin aikin banki wurin yin mu’amala da wadannan kudade.
“Bayan sun tsare ni na kwanaki 11 a jere a Jihar Legas, ba tare da na iya ganin wani daga cikin iyalina ba. EFCC din sun fada min cewa an samu karancin Dalar Amurka miliyan 40, kuma ni ake so na kawo su.
“Sun ci gaba da tuhuma ta cewa Dala Miliyan 65 ne suke nema a hannuna, ba dala miliyan 25 da na yi musu bayani ba. Masu binciken na EFCC sun sanar da ni cewa, har sai na samar da wadannan cikon kudade da suke nema kafin su kyale ni na bar inda suke tsare da ni.
“Saboda bani da wadannan kudade da EFCC ke nema, dole na iya yin karo-karo wurin hada kaso 50% na abin da suke nema. Har sai da ta kai na ci bashi a bankin da na yi aiki na ba su kudaden ta hannun lauya na. Bayan nan ne suka sake ni a ranar 20 ga watan Mayun 2016.
“Haka kuma a tsakanin makonni uku dga ranar 13 ga watan Mayu zuwa 6 ga watan Yunin 2016, suka tilasta min na kai Naira Biliyan 9.08 ga asusun tattara kudaden da aka kwato dake Babban Bankin Nijeriya.” Inji Dauda

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here