Salihu Sagir Takai ya sake komawa jam’iyyar APC

0

Salihu Sagir Takai ya sake komawa jam’iyyar APC

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano a tutar jam’iyyar PRP Malam Salihu Sagir Takai, ya fice daga jam’iyyar sa ta PRP zuwa jam’iyyar APC.

Sanarwar hakan ta fito daga bakin mai taimaka masa a harkokin yaɗa labarai Abdullahi Musa Huguma, a lokacin da ya ke zantawa da jaridar Nigerian Tracker.

Abdullahi Musa Huguma ya ƙara da cewa Salihu Sagir Takai ya yanke shawarar komawa jam’iyyar APC ne bayan ya tattauna da abokan siyasar na ƙananan hukumomi 44, da malaman jami’o’i da kuma malaman addini waɗanda su ke cikin tafiyar tun daga shekarar 2011.

See also  FG Reiterated Commitment to Infrastructure in Major Highways and Institutions

Haka kuma Abdullahi Musa Huguma ya ce magoyan bayan Salihu Sagir Takai sun cimma matsayar shiga jam’iyyar APC

Idan za a iya tunawa dai a cikin shekarar 2018 ne Salihu Sagir Takai ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP sakamakon zargin rashin adalci da ya ce ake yi a jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here