GWAMNA GANDUJE ZAI MAYAR DA GIDAN JARIDAR TRIUMPH KASUWAR CHANJI
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yana duba wata shawara da wani kamfani mai zaman kansa ya bayar ta mayar da harabar Kamfanin Jaridar Triumph zuwa Kasuwar Canjin Kuɗaɗen Ƙasashen Waje, a cewar jaridar Intanet, Kano Focus.
Wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Huɗda da Jama’a na Fadar Gwamnatin Kano, Aminu Kabir Yassar ya fitar ranar Laraba ta ce Gwamna Ganduje yana kuma duba yiwuwar mayar da Otal ɗin Daula zuwa gidan zama.
Sanarwar ta ce kamfanoni biyu – LAMASH Properties Limited da FARI Properties Limited – sun gabatar da shawara ga Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano bisa tsarin “Build-Operate-Transfer”.
Shi ma a na sa jawabi a madadin LAMASH Rabi’u Sa’id, ya ce kamfaninsa zai yi amfani da harabar “Gidan Sa’adu Zungur” ta Kamfanin Jaridar Triumph don samar da “Kasuwar Canjin Kuɗaɗen Ƙasashen Waje”.
Mista Sa’id, wanda Injiniya ne ya ce kamfaninsa zai samar da cikakken tsaro da sauran abubuwan more rayuwa kamar yadda ake samu a biranen da ake hada-hada kamar Legas ko Dubai.
Haka kuma, wakilin FARI Properties Ltd., Abdulkadir Abdulkadir, ya gabatar da shawarar samar da gida na alfarma mai cin iyali 57 da kayan more rayuwa a harabar Otal ɗin Daula.
“Yayinda gwamnati za ta samar da fili a matsayin kadara, kamfaninmu zai samar da kuɗaɗe da ƙwararru don gudanar da aikin”, in ji Mista Abdulkadir.
Da yake maraba da waɗannan shawarwari, Gwamna Ganduje ya ce ya damu da yanayin tsaro a Kasuwar Canjin Kuɗaɗen Ƙasashen Waje ta WAPA, wadda take kusa da Kamfanin Jaridar Triumph, wanda yake aiki a tsittsinke.
“Kamfanin Jaridar Triumph yana buƙatar waje mai faɗi a muhalli mai nutsuwa da kayan aiki na zamani don mayar da shi kamfanin gwamnati da zai iya jurar wahala”, in ji Gwamna Ganduje.
Idan dai ba a manta ba, ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaɓen 2019 a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya maka gwamnatin Gwamna Ganduje a kotu bisa shirinta na cefanar da gine-ginen gwamnati.
A martaninsa, Gwamna Ganduje ya ce gwamnatinsa tana mayar da gine-ginen gwamnati ne da aka yi watsi da su zuwa abubuwan amfani.
“Maimakon barin gine-gine masu amfani su lalace, muna duba shawarar yadda za mu mayar da su ayyuka da za su canza tsarin Kano su kuma riƙa samar da kuɗaɗe ga jihar.
“Saboda haka ‘yan adawa ba za su hana mu cimma burinmu ba”, inji Gwamna Ganduje.