Babbar Sallah: GWAMNA GANDUJE YA SAKI FURSUNONI 29 A KANO
Daga Ibragim Hamisu, Kano
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya saki fursunoni 29 da ke zaman gidan gyaran hali na Dutsen-Goro a Kano.
Gwamnan da ya bayar da umurnin sakin fursunonin a yayin da ya kai ziyara gidan gyaran halin a ranar Juma’a ya ce ya aikata hakan ne saboda bikin babbar Sallah.
Gwamnan ya ce an yi la’akari da irin laifukan da suka aikata da kuma alamun sauyin halayensu yayin zamansu a gidan gyaran halin.
Ganduje ya shawarci fursunonin da aka saki da kada su sake aikata wani laifi da zai sa su sake dawowa gidan.
Ya ce za a bawa kowannensu N5,000 da zai yi amfani da shi a matsayin kuɗin mota don ya koma garin su.
Shugaban gidan gyaran halin, Abdullahi Magaji ya yabawa Gwamna Ganduje saboda sakin fursunonin.
Magaji shima ya shawarci waɗanda aka saki da su zama masu halaye na gari ta yadda ba za su sake dawowa gidan gyaran halin ba.
Mataimakin Gwamna Alh. Nasiru Yusuf Gawuna da wasu ƴan fadar gwamnati ne suka yi wa Ganduje rakiya zuwa gidan gyaran halin.