GWAMNATIN KATSINA NA KULA DA KANANAN HUKUMOMI SOSAI.

0

GWAMNATIN KATSINA NA KULA DA KANANAN HUKUMOMI SOSAI.
~~~~Inji Kwamishinan Kananan Hukumomi

@Jaridar Taskar Labarai

Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Katsina Alhaji Yau Umar Gwajogwajo ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Katsina na kiyaye da bin dokokin kashe kudi na kananan hukumomi kamar yadda suka zo a tsarin mulki da kuma dokokin kasa.

Kwamishinan na wannan bayani ne a wani taron manema labarai da ya kira a ofis nasa a karshen makon nan da muke a ciki.

Kwamishinan yace tun da na zama kwamishinan gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari bai taba yi mana katsalandan ba, ko ya sanya mu yi wani abin da yasaba wa doka a tafiyar da ma’aikatar kanana hukumomin da masarautu, ya kara da cewa ban kuma iske wani rahoton yin haka a baya ba.

Kwamishinan ya kara da cewa, tafiyar da kananan hukumomi tana da dokokin da suka kafa su da hukumomin sa ido na kudi dake kula da ana binsu don haka ana bin sau da kafa wadannan tsari wanda aka amince da shi a duk kasa ba Katsina ba.

Kwamishinan ya kara da cewa babbar nasarar da gwamnan Katsina yayi shi ne na tsayawa tsayin daka cewa dole ne, kowace karamar hukuma ta samu albashinta.

Wanda inda an kyale abin sakaka ba tsari da sanya ido da a jihar Katsina kana iya samun wata karamar hukuma na iya albashi wata bata iya wa.

Kuma a baya an yi zamanin da abin da kananan hukumomin ke samu wasu sai jiha ta taimaka masu, akan iya yi masu Albashi.

Kwamishinan ya kara da cewa, duk wani aiki da aka amince sai kananan hukumomi sun bada tallafi duk inda za ayi aikin ba a taba kasa a guiwa ba, kuma jama’ar da ake aikin don su suna gani a aikace.

Kwamishinan ya kara da cewa kofar ma’aikatar a bude take duk mai bukatar wani bayani akan yadda ake tafiyar da ma’aikatar a bisa doka yazo ko ya rubuto ko ya aiko za a saurareshi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here