NASARORIN DA MUKA SAMU.A YAKI DA TA ADDANCI A YANKIIN ZAMFARA DA KATSINA
daga Aminu iliyasu
Aranar 6 Yuli 2020 ne dai Shugaban Hukumar Sojan Kasa ta Najeriya, Laftana Janar Tukur Yusufu Buratai ya kaddamar da rundunar Operation SAHEL SANITY a wani bangare na bukukuwan shekara na hukumar sojin da ya gudana a wannan sananin soja da muke ciki a garin Faskari, Jihar Katsina. Dalilin Kaddamar da wannan rundunar dai shine domin ta tallafawa rundunar Operation HADARIN DAJI wajen kawar da miyagun ayyukan yan bindiga, barayin dabbobi, masu garkuwa da mutane, kashe – kashe da sauran illoli ga jama’a mazauna yankin.
Babu shakka mazauna yankin Arewa maso Yamman kasar nan na iya ji da kuma ganin muhimman nasarori da aka cimma da taimakon su a dan lokaci kankani. A cikin wannan gajeren lokaci 6 – 31 Yuli 2020, zaratan sojojin rundunar Operation SAHEL SANITY sun gudanar da kwantan bauna tare da fatattakar yan bindiga daga guraben buyansu a dazuzzukan jihohin Sokoto, Katsina da Zamfara. Haka kuma sojojin sun ceto wandanda ake garkuwa dasu tare da kwato shanun sata da kuma kame yan bindiga da ma masu basu bayanan sirri.
Bugu da kari, sojojin sun sami nasarar kama miyagun makamai da alburusai tare da Babura da sauran kayan amfani daga hannun yan bindiga.
Kawo yanzu, dakarun Operation SAHEL SANITY sun yi nasarar halaka yan bindiga 80, gami da kwato shanu 943, da kananan dabbobi 633, Haka kuma sun damke yan bindiga 33, tare da cafke bindigu kirar AK 47 guda 7, bindiga mai barin wuta – GPMG – 1 da kuma bindigu kirar gida – 16.
Haka kuma an kubutar da mutum 17 da ake garkuwa da su tare da cafke masu baiwa yan bindiga bayanai su 14. A yayin haka, Sojojin sun murkushe tare da lalatar da guraben yan bindiga da dama. Za’a iya cewa dai rundunar Operation SAHEL SANITY ta cimma nasarori masu yawa daga lokacin kaddamar da ita.
Duk da haka, zaratan sojojin na ci gaba da mamaye dukkan guraren da ake tsammanin yan bindiga gami da gudanar da sunturi da kwantan bauna domin kawar da baragurbi. Wannan yanayi a bayyane yake idan aka kula da yadda manoma, da sauran jama’a ke gudanar da al’amuransu na yau da gobe cikin walwala.
A wannna gaba, Shugaban Hukumar Sojojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai na yabawa sojojin kan nasarorin da aka samu a wannan takaitaccen lokaci ya kuma bukace su da kada suyi kasa a gwiwa. Bugu da kari yana mai mika sakon fatan alheri na bikin Sallah babba ga jama’ar yankin Arewa maso Yamma tare da jaddada musu tsayaicin hukumar soja don kawar da duk wasu miyagu daga yankin.
Wadanda aka kama
AMINU ILIYASU
Colonel
Nigerian Army Operations Media Coordinator
1 August 2020