ADDU’A NA AIKI: MAYAKAN DAJI NA CIKIN FIRGICI

0

ADDU’A NA AIKI: MAYAKAN DAJI NA CIKIN FIRGICI

@Taskar Labarai

Majiyoyi masu tushe dake da alaka da barayi masu dauke da makamai a dazuzzukan rugu suna a cikin kidima da rudewa, kuma sun rasa kumajin haduwa don kai wani mummunan Hari.

Majiyarmu ta tabbatar mana cewa manyan su, wadanda ke haduwa don yanke shawarar ya zasu kai hari wanda zai tada hankali duk sun boye kuma suna tsoron haduwa waje guda.wasu sun ce sun bar yankin.ko kuma ba Wanda yasan ina suke.

Majiyarmu ta tabbatar mana cewa, da yawan manyansu basu yarda da ko sauran na tare dasu, amma sun boye kansu sai amintattunsu kawai ke iya ganin su, suyi magana dasu.

Majiyarmu tace sun yanke duk wata waya ta hannu ko yarda da wani alaka ta karfen bature kamar rdio da sauransu,suna boye suna amsar bayanai daga na kusa dasu. ta tsohuwar hanya baka da baka.

Majiyarmu ta tabbatar mana cewa sun bar yawo a cikin gungu mai yawa don tsoron harin sama, da aka iya kawo wa irin haduwar tasu.

Mun samu tabbacin sam soja basu kashe Sani Dangote ba wanda yake rike da dajin iyaka da Jibia da kuma Birnin gwari.

Majiyarmu ta tabbatar mana Dangote ya gane za a kai masa harin sama ko ta kasa don haka sai ya raba mutanensa kashi-kashi shi kuma ya janye wasu da ya amince dasu ya boye.

Majiyarmu tace daga baya ya koma shi kadai ya rika yawo a dajin cikin sanda, masu gadinsa na nesa nesa don kauce ma harin sama ko na kwantar bauna.

A haka ya sulale ya shiga wani bangare na dajin Zamfara, wasu sun ce ya shiga kasar Nijar, amma bayan fitar da sanarwa soja, ya aiko da sako ga mutanensa cewa yana da rai, sai dai yana basu shawarar kowa ya nemi mafaka don sa’a ta juya masu baya.
wata majiyar tace don ya tabbatar masu yana da rai ya shigo dajin dumburun a satin da ya wuce,mai fada mana yace “” ya rika ganawa da amintattunshi a dai dai ku kuma ya gama ya koma in da ya fito”” inji wani da ya tabbatar da abin da ya faru.

Majiyarmu tace dajin ya rude babu wani takaimamen jagora a cikin barayin don babu wanda ya san ina ogansa yake.

Majiyarmu tace hare-haren da ake samu a wasu yankuna kananan mahara ne, wadanda ke cikin bukata kuma suke cikin takura da matsi, su kan tunzura su fito su kai farmaki su koma daji.

A tsakanin Jibia zuwa Dandume ta jihar Katsina, ada akwai sama da mutane dari uku ana garkuwa da su, yanzu ko basu da yawa.

Maharan yanzu in sun shigo ta abinci suke da nama da kudi nan da nan, ba su saci mutum ba, sai an yi kwanaki.

Wani masanin harkar tsaro mai suna Dakta RB Hosfal yace, “a yanayin irin wannan da mugu ya shiga rudu a hakan akan karfafawa al’umma yadda zasu kare kansu da daukar matakan ko ta kwana. A kuma irin wanna yanayin in wasu daga cikin miyagun suka ce suna neman a zauna dasu akan iya sauraren su a matakan tsaro da soja ba siyasa ba”.

Watau magana ce, wadda jami’an tsaro za suyi da miyagun ba wai shugabannin siyasa ba, in aka yi hakan to wadanda suka bada hadin kai suna iya kara taimakon jami’an tsaron.

Taskar Labarai ita ce jaridar da ta kwashe sama da shekaru biyu tana bada labaran musamman akan halin da tsaro ke ciki a yankin arewa maso yamma, kuma bata taba kuskuren hasashe ba. tana da masu bata ingantattun bayanai a fagagen daban-daban kuma ba a taba samun ta da karya ba.
________________________________________________
Taskar labarai na bisa yanar gizo ta www.taskarlabarai.com tana yar uwarta turanci akan www.thelinksnews.com duk sako ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here