GUDUMMUWARMU GA GREEN HOUSE KATSNA

0

GUDUMMUWARMU GA GREEN HOUSE KATSNA

Daga Danjuma Katsina

A shekarar 2001 aka kafa cibiyar horas da matasa ta Vocational Training Centre. Wadda marigayi Alhaji MD Yusufu ya dau nauyin assasata.

Da za a sayi kayan horaswa na fadawa wadanda na zabo su taimaka mani Alhaji Aminu Tukur Unguwar Jaji da marigayi Alhaji Bashir Imam da Abdulmalik Sani cewa, duk kayan da za a saya a rika sayensu a Katsina wajen ‘yan kasuwanmu don su ma a taimaka masu.

Zamu sayi kekuna da injinan saka da wasu kayayyakin Alhaji Aminu Tukur Unguwar Maji yace ai duk kayan dinki da saka wajen wani da ake kira Alhaji Shehu Maizare bakin kasuwa za a saya, lokacin yana da shago a bakin tsohuwar kasuwa.

Ya shiga fadin halayyar kirkinshi, nace na amince,
Da Aminu ya dawo daga sayen kaya wajenshi yace farin cikin shi shi ne Alhaji Shehu yaji dadin cinikin, a 2001 Lokacin ‘yan siyasa basu fara sayyar riya suna rabawa ba. Muka sayi kayan dinki da saka na kudi masu yawa.
Tun daga lokacin duk shekara duk sayen kayan dinkin da zamu yi mu raba ma dalibai, su yi sana’a a can mu keyi.
A kalla duk lokacin yaye daliban mu muna rabar da keken dinki dari, duk wanda zai saya ya saya ya bamu can muke tura shi.
Hakan kuma mun rika tallar shagon mai zare duk Wanda ya ce mana ina muke sayen kaya? Sai mice shagon Alhaji shehu mai zare,daga baya kuma da ya bude green house muka rika tallar cewa a green house ne.
Mun tallata Green house sosai.saboda muna jin dadin hudda dasu.kuma muna ganin gudummuwar mu kenan na habaka wajen.

Duk tsawon shekarun nan ban taba zuwa neman inga waye Alhaji Shehu Maizare ba, ban kuma taba neman wata alfarma ko gudummuwa a wajen shi ba, ban san shi ba ido da ido ba..
Amma ya kanyi mana ragowa in zamu yi sayayya.a matsayin tsaffin kwastomomi kuma ya kan bada keke daya a baiwa daliba mafi zarra.

Ban taba ganinsa ba, sai a taro da na hango shi bisa babban tebur a wajen karrama su Yusufu jargaba. Da Alhaji dahiru sarki.Ko a lokacin ban samu gaisawa dashi ba, na hange shi kawai zai shiga mota,.
Ama Naji dadi kwarai da gaske.domin kamfanin
Green House sun yi mani abubuwa guda biyu da naji dadinsu na farko shi ne sun dauki wasu tsaffin daliban Vocational Training Centre suna masu aiki yanzu haka.

Na biyu sun karrama Aminai na guda biyu, Yusufu Ibrahim Jargaba da kuma Alhaji Dahiru Usman Sarki. Allah ya saka da alheri.
Allah kara dauka kamfanin Wanda yake alami ne na alfahari da farin cikin duk wani bakatsine.
Danjuma katsina
Shine shugaban cibiyar horas da matasa ta MDYUSUFU. Mai suna katsina vocational training centre. Dan jarida ne ,mawallafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here