YADDA AKE BAUTAR DA MALAMAN MAKARANTA DA BASHI A KATSINA

0

BINCIKEN MUSAMMAN: YADDA AKE BAUTAR DA MALAMAN MAKARANTA DA BASHI A KATSINA

Daga Taskar Labarai

Mun gudanar da wani bincike akan yadda ake maida wasu ma’aikata bayi da bashi a jihar Katsina musamman malaman makaranta da kuma na kiwon lafiya.

Binciken mu yafi dogara kacokam akan malaman makarantun firamare da sakandare. Mun gano da yawa daga cikin malaman nan suna koyar wa ba cikin hayyacinsu ba, saboda zullumin tashin hankalin bashin dake bisa kansu.

Mun gano da yawa suna safa da marwa tsakanin gidan sarki da wajen ‘yansanda da kotunan Alkalai don matsalar bashi da ta dabaibaye su.

Mun samu tabbacin bashin duk ana basu shi ne da ruwa kuma ruwan sai yayi ta hauhawa daga nan sai ya kai biyanshi sai illa masha Allah.

Mun gano a wasu kananan hukumomin da sa hannun kungiyoyin malaman makarantu da kuma ES ES ake wa malamai wannan kamun kazar kuku.

Mun gano wannan halin da malamai kan shiga kan sanya yana taba kwanciyar hankalinsu kuma har ya shafi tsayawa a tsanake su koya wa daliban.

Yadda ake bada bashin yana da hanyoyi daban-daban, daga cikinsu za a zo da shinkafa ta saidawa misali ace buhu daya akan naira dubu Goma sha biyu sai a saida wa malami akan dubu ashirin sai kuma a saya wajen shi akan dubu Goma, nan take an dora wa malamin makaranta dubu Goma akan bashin dubu Goma.

Ko kuma za a zo da kudi lakadan sai ace za a bashi naira dubu dari da arba’in akan naira dubu dari biyu da sittin na mashin an dora masa naira dubu dari da ashirin akan bashin naira dubu dari da arba’in.

Wadannan misalai biyu kacal ta hanyar da ake dabaibaye malami da bashi, banda bashin banki da kullum ake masu romon baka kuma ana sanya wa suna karba.

See also  ‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Hakimi Yankan Rago A Kebbi

Mun gano duk shekara haka kawai sai malamai su wayi gari suga an cire masu wani abu cikin albashi suyi ta zarya wasu sai dai suyi Allah ya isa, duk shekara hakan na faruwa a tsakiyar shekarar kowace shekara.

Ana zargin wasu shugabannin kungiyar malamai ne, in sun ci bashi ko suna neman wasu kudi sai su hada kai suyi wannan cutar.

Mun kasa tabbatar da zargin don wasu shugabannin kungiyar malamai da muka yi magana dasu sun karyata.

Duk shekara akan samu masu cin bashin nan an wazge masu wasu kudi ace sun ci bashi, ayi ta zarya don a gyara har mai bi ya hakura yayi Allah ya isa.

Wani kuma in yana nesa, in ya ga wahalar da zai sha ta bin a gyara, sai ya hakura, misali wanda ke Dandume, ko sabuwa.
Mun gano hukumar ilmin firamare ta jiha bata da hannu a irin wannan badakala, sun ma taba yunkurin su taka ma abin burki ya gagara.

Lokaci-lokaci daga ofishin ES na kananan hukumomi za a rubuto ma hukumar kula da makarantun firamare na jiha sunayen wadanda ake bi bashi da yadda za a cire bashin, hukumar ta jiha ba yadda ta iya dole ta bi rubutun da aka aiko mata.

Za a tattara wadannan kudaden da aka ciccire kowane ES ya yi bayanin yadda za a yi dasu.

Wasu da jaridar nan ta zanta dasu sunyi kira ga hukumar ilmin firamare ta jiha da ta bullo da wani tsari da zai kare malamai daga fada wa dabaibayin bashi su zama bayin ‘yan bashi.
________________________________________________
Taskar labarai na bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com da ‘yar uwarta Turanci dake akan www.thelinksnews.com. duk sako a aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here