YAN FASHIN DAJI SUN HALLAKA SHUGABAN MATASAN JAM’IYYAR APC (YOUTH LEADER) DA WASU MUTANE BIYU A BATSARI.

0

‘YAN FASHIN DAJI SUN HALLAKA SHUGABAN MATASAN JAM’IYYAR APC (YOUTH LEADER) DA WASU MUTANE BIYU A BATSARI.
@ jaridar taskar labarai

Da misalin karfe 12:30am na daren litanin 03-08-2020 wasu ‘yan bindiga suka shiga kauyen Garwa dake cikin yankin karamar hukumar Batsari, inda suka kai samame gidan wani bawan Allah mai suna Sadi wanda shi ne shugaban matasan jam’iyyar APC na Yau-yau/mallamawa ward.

Sun bindige shi har lahira sai dai wata majiya ta bayyana cewa basu saci komai ba kuma ba suyi wa kowa komai ba kawai sun je kashe shi ne kuma da suka gama aika-aika sun bar garin salin alin.

Haka kuma, sun harbe wani matashi mai suna Abdulhadi Husamatu a kauyen Saki Jiki yayin wani dauki da suka kai lokacin da ‘yan bindiga suka sato shanu daga kauyen Tudun Wada sai kawai su ka yi harbin kai mai uwa da wabi wanda yayi sanadiyyar rasuwar shi.

A ranar alhamis da dare 30-07-2020 sun je wani gidajen Fulani dake arewacin Kurmiyal, Hayin Tazar sun iske wani Bafullatani a gidansa Sani Makarme suka tambaye shi inda shanunshi suke da yaki fadi masu sai su ka ce tun da kafi son shanunka da ranka bari mu kashe ka, haka kuwa aka yi suka harbe shi nan take.
Yanzu barayin nan sun koma harin daukar fansa da fashi da satar abinci da shanu.tun da manyansu suka bace sai yaran Kan kai samame.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here