Dauda Lawal Ya Mayar Wa Da Ibrahim Magu Martani Mai Zafi

0
351

Dauda Lawal Ya Mayar Wa Da Ibrahim Magu Martani Mai Zafi

Tsohon Babban Daraktan Bankin nan na ‘First Bank of Nigeria Plc’ Dr. Dauda Lawal ya mayar da martani ga tumbukakken tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu.
Dakta Dauda Lawal (Gamjin Gusau) ya mayar da wannan martanin ne a cikin takardar da ya aikewa da Kwamitin Shugaban Kasa wanda ke bincikar badakalar da ake zargin Magu da aikatawa.
Takardar wacce manema labarai suka samu kwafinta a yau Alhamis a Abuja, Dauda ya bayyana cewa bayanan da Magu ya aike wa kwamitin babu komi a ciki face karairayi da kokarin rufe gaskiya.
Haka nan kuma a cikin takardar, Dauda ya zargi Magu da kokarin kirkirar karairayi domin ya hana kwamitin fahimtar hakikanin gaskiya.
A cikin martanin na Dauda Lawal, ya ce: “Kiri-kiri Magu ya kasa yin lissafi daidai. Domin ya ce, an karbo Dalar Amurka $153,310.000 daga Kamfanin NNPC a madadin Misis Diezani Alison Madueke, wanda kuma a jerin sunayen mutanen da suka amso kudin idan ka hada jimilla za ka ga kudin ya kama Dala $152,480,000. Wannan ba komi ba ne face rashin gaskiya daga wurin Magu.
Martanin na Dauda Lawal ya zo ne a kasa da mako guda da Ibrahim Magu ya fitar da wata takarda kan zargin rashawa, wulakanta ofis, danniya da zalunci da ake yi masa, inda tumbukakken tsohon shugaban na EFCC ya kawo batutuwa kan Dauda Lawal.
Sai dai a cewar Dauda Lawal, a gabadaya abubuwan da Magu ya rubuta tufka da warwara ne kawai ya yi a kansa. Hatta adadin kudaden da ya ke fadi sun saba daga asalin tuhumar da suke masa na farko. Sannan kuma sun gaza kawo shaida kan yadda ya amshi kudaden da yadda ya kashe su.
Da karshe, Dauda ya karyata Magu kan zargin da ya yi na cewa, wadanda ake zargi a kes din Misis Diezani suna haifar da tsaiko da gangan a shari’ar da ake yi. Inda tsohon shugaban bankin ya ce, “Wannan ma karya ne. Domin a bayyana ya ke cewa a kodayaushe a ka neme ni ina bayyana a gaban kotu, ba a taba samun rana guda da na yi fashin halartar zaman kotu ba. Don haka ba gaskiya ya fadi ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here