JAMI’AR BAYERO KANO TA YI SABON SHUGABA
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
An bayyana Farfesa Sagir Adamu Aliyu na tsangayar Ilimi a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar zama shugaban jami’ar Bayero Kano bayan fafatawa da aka yi tsakanin ‘yan takara.
Farfesa Sagir ya yi nasarar zama shugaban jami’ar ne bayan ya samu kuri’u 1026, yayin da Farfesa Tanko Adamu ya zo a matsayi na biyu da kuri’u 416, Sai kuma Farfesa M.D Mustapha da ya zo na uku da kuri’u 10 kacal.
Wannan sakamakon ya nuna cewa Farfesa Sagir Adamu ya zama zababben shugaban jami’ar ta Bayero wato (Vice Chancellor) bayan Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya cika wa’adinsa.