“MAIBA GWAMNAN JIHAR KATSINA SHAWARA KAN HARKAR TSARO YAYI TARON MANEMA KAN ZAGAYEN DAZAI FARA NA KANANAN HUKUMOMIN DAKE FAMA DA MATSALAR A JIHAR KATSINA

0

“MAIBA GWAMNAN JIHAR KATSINA SHAWARA KAN HARKAR TSARO YAYI TARON MANEMA KAN ZAGAYEN DAZAI FARA NA KANANAN HUKUMOMIN DAKE FAMA DA MATSALAR A JIHAR KATSINA”.
============================================

“Maiba Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari shawara kan harkar tsaro Alh. Ibrahim Katsina yayi taron manema labarai dazai fara zagayawa, a kananan hukumomin dake fama da matsalar tsaro a Jihar Katsina”.

“A lokacin taron manema labaran Maiba Gwamnan Shawara “ya bayyana irin nasororin da aka samu a Jihar Katsina kan aikin samar da tsaro da Jami’an tsaro Sojoji da sauran ma’aikatan tsaro suke cikin yi”.

“Maiba Gwamnan Shawara ya nuna jin dadin shi da jinjina ga Jami’an tsaron kan yadda suke aiki ba dare ba rana wajen aikin samar da tsaro a Jihar Katsina. Kuma, “Alhamdulillahi. Tsaro yana samuwa bakin gwalgwado a Jihar Katsina, al’amurra sun fara daidaita, Al’umma sun fara komawa rayuwar su ta zaman lafiya kamar da”.

“Harkar tsaro harka ce ta kowa da kowa idan jama’a suka bada hadin kai da goyon baya aka hada hannu da karfe, insha Allahu nan bada dadewa ba komi zaya zama tarihi, Jihar Katsina ta koma kamar da yadda aka santa da zaman lafiya”.

“Daga karshe Maiba Gwamnan shawara “ya godema yan jarida kan yadda suke bada gudumuwa wajen wayar da kan Al’umma kan matsalar tsaron nan, harkar wayar dakai na yan jarida yana taimakawa kwarai da gaske wajen dakile matsalar tsaro a Jihar Katsina dama kasa baki daya”.

“Makasudin zagayen kananan hukumomin dake fama da matsalar tsaro a Jihar Katsina da Maiba Gwamnan Shawara zai fara, don tabbatar ma duniya “cewa harkar tsaro a Jihar Katsina ta fara inganta, al’ummomin yankunan da matsalar ta shafa sun fara komawa gudanar da rayuwar su cikin zaman lafiya”.

“Saboda samuwa da tsaron ya fara mazauna yankunan da abun ya shafa mafi yawa sun koma gonakin su, suna noma daminar nan ta bana”. “A bisa yadda aikin samar da tsaron yake tafiya a halin yanzu nan bada jimawa ba za’a kawo karshen yan ta’adda Barayin Shanu da yaddar Allah”. “Allah ya bamu zaman lafiya mai dorewa”.

Taron manema labaran ya gudana a ofishin Maiba Gwamnan Shawara, ya kuma samu Halartar jami’,in hudda da Jama’a (PRO) n rundunar Yan sanda ta Jihar Katsina ASP. Gambo Isah, sai mai taimaka Maigirma Gwamnan Jihar Katsina na musamman kan harkar tsaro Hon. Umar Gambo Kofa. Da sauran manema labarai”.

Rahoto. Surajo Yandaki
Mobile Media Crew
06, AUGUST 2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here