Yadda ‘Yan Bindiga Suka Yi Shigar Mata Da Abayoyi Suka Sace ‘Yar Shekara 11 Da Matar Aure Mai Yara Bakwai A Cikin Garin Kurfi Ta Jihar Katsina

0

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Yi Shigar Mata Da Abayoyi Suka Sace ‘Yar Shekara 11 Da Matar Aure Mai Yara Bakwai A Cikin Garin Kurfi Ta Jihar Katsina

…yadda mu ka yi kokowa da ‘yan bindiga har na kubuta a hannun su

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

A daren jiya ne, ‘yan bindiga dauke da bindigogi, suka kai hari a cikin garin karamar hukumar Kurfi, inda suka Yi awan gaba da yarinya yar shekara goma sha daya, Khadija Muttaka Mamman, wada diya ce ga Dakta Muttaka Mamman, Shugaban sashen kula da dalibai na jamiar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsinma da kuma wata matar aure, Murja Umar Faruq mai yaya Bakwai.

A wata ziyara da RARIYA ta kai a karamar hukumar Kurfi, domin gano yadda yan bindiga suka kai harin a daren jiya.

Dakta Muttaka Mamman, wanda aka sace wa diya, Khadija, ya bayyanawa RARIYA cewa sun zo ne da misalin karfe tara da mintin ashiri, kuma sun zo ne sanye da abayoyi, a kasa suka zo. Sun fizgi diyata daga hannun dan uwanta, kuma sun saci matar makwabcina, sun kuma harbi wani mai shago, wanda yanzu haka yana kwance a asibitin nan garin Kurfi.

Muttaka Mamman ya kara da cewa har zuwa maganar da muke da kai yanzu suna hannun su, lokacin da suka zo Ina nan cikin gida, an tura shi ya je ya taho da Khadija. Labarin da muke samu sun kai su ashirin, amma sun ajiye mashinan a wajen gari. Muna dai ta addua Allah ya bayyanar da su. Bikin diyar yayana mu ko zo, an daura aure shekaran jiya, jiya aka yi walima. Yau mu ke son komawa Dutsinma, haka dai Allah ya kaddara, amma wannan bai rasa nasaba da ma su kai masu bayanai.

Malama Shamsiya Umar, wadda ta kwaci kanta a hannun su, bayan sun yi kokowa ta bayyanawa RARIYA cewa dawowarmu daga unguwa ni da maigidana, sai na ji wata irin Kara, na dauka tashin bam ne, sai ya ce bindiga ce, cikin rudani na fito waje Ina fitowa daya daga cikin su ya damke ni, saboda na fito ne don in je ga yayata da na ji tana ihun a kawo mata dauki. Bayan yin kokowar dama rigata ya rike na fizge na ruga. Wallahi jiya mun ga tashin hankali, wanda ban taba gani ba a tarihin rayuwata ba. Allah ya kubutar da Khadija da yayata hannun miyagun mutanen nan. Suna da yawa na tsorata sosai.

Shi ma Malam Ahmad A. Kurfi, wanda ‘yan bindiga suka sacewa mata ya bayyanawa RARIYA cewa lokacin da suka zo yana cikin gari, sai na ji karar harbe-harbe, sai na mike na taho unguwarmu, Ina zuwa na ga taron mutanen aka ce sun tafi da matata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here