DA MUN SO DA SAI MU MURDE ZABEN 2019

0
212

DA MUN SO DA SAI MU MURDE ZABEN 2019- in ji Buhari

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce jam’iyyarsa ta APC mai mulki ta na da ikon amfani da sojoji wajen karbe jihohin adawa a babban zaben 2019.

Jaridar The Cable ta ruwaito Shugaban kasar ya na cewa duk da damar da su ke da ita, sun zabi su yi adalci a zaben da ya gabata.

Muhammadu Buhari ya yi wannan bayani ne lokacin da ya zauna da gwamnonin yankin Arewa maso gabashin kasar nan jiya Litinin a fadarsa da ke Abuja. A ganar akwai gwamnonin PDP da suka hada da: Ahmadu Fintiri (Adamawa), Bala Mohammed (Bauchi) da Darius Ishaku (Taraba).

Buhari ya ce cewa: “Gaskiya ne mun rasa wasu jihohi a matsayinmu na jam’iyya da ke kan mulki a kasar da yanzu ta ke tasowa, wanda an saba ganin wannan.

Ina alfahari da cewa ba mu yi rashin adalci ba, wannan ya sa mu ka rasa wasu zabuka duk da mu ne jam’iyya mai mulki. Hakan ya na nufin mu na da kure-kurenmu.

Da ce mun shirya magudi da sai mu yi anfani da sojojin kasa, da ‘yan sanda da sauransu, mu cinye zaben.” inji Shugaban kasar.

Shugaban kasar ya kara da cewa: “Mu na so ne kawai mu nuna maku cewa mu na da tausayi, kuma mu ‘yan Najeriya ne. Za mu cigaba da yin bakin kokarinmu.

Daga karshe shugaba Buhari ya baiwa ‘yan Najeriya hakurin abin da ya faru a baya, ya kuma yi alkawarin gwamnatinsa za ta cigaba da yin bakin gwargwadon abin da za ta iya.

Sannan shugaban kasar ya koka game da rashin tsaron da ake fama da shi a Najeriya, kuma yayi kira ga jami’an tsaro su dage wajen ganin sun kawo zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here