Gwamnatin Kano ta yaba da yadda aka bi tsarin bude Makarantu
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru ya bayyana gamsuwasa a kan yadda shugabannin makarantun Sakandire suka bi ka’idojin kariya daga cutar COVID-19.
Malam Sunusi kiru yayin da yake rangadin duba makarantun GGSS Shekara da kuma First Lady’s collage da ke Mariri yace abin farin ciki ne ganin yadda shugabannin makarantu suke tabbatar da anbi ka’idojin da aka shimfida a dai-dai lokacin da ake daf da fara jarrabawar kammala Sakandire.
Sai ya bukaci dalibai da su bawa gwamnati hadin kai ta hanyar amfani da kayan kariya da aka basu tare da bada tazara, sannan ya bukaci su mayar da hankali kan jarrabawar su don samun sakamako mai kyau.
Kwamishinan ya yabawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda ya samar da abubuwan da ake bukata don kariya daga cutar Corona cikin gaggawa.
Sannan ya yabawa yan majalisar zartarwar jihar bisa goyon bayan su don ganin an sake bude makarantun.