GWAMNATIN KATSINA TA SAMU TALLAFIN KAYAN ABINCI DON RABA MA MASU JAMA A

0

GWAMNATIN KATSINA TA SAMU TALLAFIN KAYAN ABINCI DON RABA MA MASU JAMA A

An gudanar da taron kaddamar da rabon kayan abincin wanda kungiyoyi suka baiwa jihar Katsina domin rage radadin Corona ga masu karamin karfi, taron ya gudana ne a Central Store dake katsina.

Bayan godiya ga Allah SWT Mai girma gwamnan jihar Katsina Rt Hon Alh Aminu Bello Masari yayi godiya ga wannan kungiyoyi bisa tallafin da suka baiwa jihar Katsina domin a rabawa al’umma mabukata, tallafin ya hada da dubunnan buhunan kayan abinci da Indomie da sauran nau’ikan abinci wanda suka hada harda Garin Kwaki.

Mai girma gwamna ya ja hankulan wadanda alhakin raba wannan kaya ya hau kansu da suji tsoron Allah su raba wannan kayan abinci ga mabukata masu karamin karfi al’ummar jihar Katsina.

Taron ya samu halartar Maigirma mataimakin Gwamnan Alh Mannir Yakubu, Kakakin majalissar dokokin jihar Katsina Rt Hon Tasi’u Musa Maigari Zango, Sakataren gwamnatin jihar Katsina Dr Mustapha Inuwa.

Kwamanshinan ma’aikatar kananun hukumomi da masarautun gargajiya na jihar Katsina Rt Hon Ya’u Umar GwajoGwajo, Kwamanshinan ruwa Hon Musa Adamu Funtua, kwamanshinan shari’ah Barr Elmarzuq, Mai ba gwamna shawara kan ilimin ‘ya’ya mata Haj Amina lawal Dauda Mani, da wasu daga cikin masu rike da mukaman gwamnati.

Abubakar Shafi’i Alolo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here