NASARORI SOJOJI A YAKI DA BARAYIN DAJI A YANKIN AREWA MASO YAMMA.

0

NASARORI SOJOJI A YAKI DA BARAYIN DAJI A YANKIN AREWA MASO YAMMA.
Daga Ibrahim Hamisu Kano
@ jaridar taskar labarai
1. A kokarin da ake na kawar da masu satar shanu da sauran muggan laifuka a yankin arewa maso yamma, dakarun oparation sharar daji ta samu nasarori masu yawa a wannan yaki da take kamar haka.

2. A ranar 5 ga watan ogas 2020, dakarunmu da ke karamar hukumar Batsari sun dakile wani hari da aka kaiwa mazauna garin Zamfarawa da ke kauyen Kagara.
Masu satar shanun sun mamaye kauyen sannan suka sace shanu masu yawa, yayin da suke kokarin kubuta, tawagarmu ta dira a gun inda ta farma masu, muka hallaka wasu wasu kuma suka samu raunuka, sannan muka mayar da dukkanin shanun ga masu shi,

3. Haka a ranr 6- ga augusta 2020, tawagar Dakarunmu mai suna Dangulbi sun kama Rabiu Salisu, wanda shi ne mai masu leken asiri a wannan yankin, haka kuma dakarunmu sunyi sansani a Bagega inda muka kama barayin shanu guda biyu Sani Sani da Sani Abubakar da suka kware wajen sayen shanu da kayayyakin da aka sato.

4. Haka kuma dakarunmu sun kwato Shanu 17 daga hannun masu satar shanu a kauyen Dogon Ruwa.

5. A wata fita rangadi da dakarunmu sukai, mun kama Saifullahi Adamu wanda shi ne dan leken asiri kuma mai yi wa Barayin shanu safarar kayayyaki a garin Garin dogo da ke jihar Katsina. Saifullah an kama shi ne shi da matar HauwaAbubakar da ya tilasta mata ta aure shi, wanda ya zuwa yanzu an kubutar da Hauwa Abubakar, kuma an damkata ga gwamnatin jihar Katsina.

6. A ranar 7 ogas 2020 dakarunmunmu sunyi sansani a garin Anka, a wani samame da mu kayi mun kama mutum biyu da ake zargin bayarin shanu ne, Abdulaziz da Ismaila a kauyen Malamawa, da ke karamar hukumar Anka, mun kama su ne da taimakon wadanda ake sayarwa da shanu, sannan dakarunmu sun kama wasu barayin Shanu Hassan Malam, da Kabiru Ahmad da surajo Muhammad a sabon birnin da kauyen Munhaye a hanyar magami Road dake jihar Zamfara.

7. A ranar 7 ga watan dai dakarunmu sun yada zango a garin Tsafe da ke jihar zamfara bayan labarari da muka samu na barayin shannu da suke taasa a yankin, mun samu nasarar kwace shanu guda 8 ba tare da bata lokaci ba muka damka su ga masu shi. A wanan ranar ta 7 ga wata, mun kama Sabiu Sani wanda bincike ya tabbatar da cewa yan sakai sun taba kama shi amma ya gudu. Sannan wani samamen da muka kai a Faskari mun kama barayin shanu guda 5 da shudiyar mota mai lamba 107 BAK, wadan da ake zargi suna hannunmu a na yi masu tambayoyi.

See also  AN SACE KANWAR SANATAN BAUCHI

8. A ranar 8 ga wata kuma dakarunmu sun kama wani kasurgumin Barayon shanu Sallau Rabiu a kauyen Natsinta tare da shanu 3, sannan dakarunmu sun yi nasara wani barawon shanun mai suna Usman sulaiman, wanda ake zargin an kama shi ne a lokacin da kokarin shiga kauye neman abinci, ya tabvatar da cewa yana cikin yan taadan da suke taadanci a yankin Batsari ta jihar Katsina.

9. A ranar 9 ga watan Agusta dakarunmu sun samu nasarar kama barayin shanu guda 2 da suka addabi yankin Danmusa da Runka da suka hada da Jamilu mani, da Aminu Lawal.
Sannan dakarunmu sun kama wani dan taadan mai suna Sani Saidu yana sanye da kayan ‘yan sanda, inda ya sauya suna zuwa James Oname, wanda bincike ya tabbatar da cewa an kashe shi tun shekara 2015 a hannun Barayin shanu, da ke Tungar Rakumi a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara. Haka kuma dakarunmu sun lalata sansanin yan taada da fitaccen barawon shanon nan Abu-Radde ya ke jaronta a yankin Batsari, inda muka kama bindugu guda 4 da sauran kayayyaki.

10. Haka kuma a ranar 10 ga watan agusta 2020, Dakarunmu sun samu nasarar kubutar Auwal Yusuf a tsakanin hanya garin Yarsanta zuwa Kabuge, haka kuma sintiri da tawagarmu ta yi a kan hanyar Bagega zuwa sabon birni inda mukai arangama da barayin shanu, kuma mukai nasarar kwato shanu guda 4.

12. Babban hafsan hafsoshin sojojin Nigriya General Tukur Yusuf Burutai ya yaba da irin wannan nasarori da dakarun sojoji Nigeriya suka samu a yanki arewa maso yamma. sannan ya tabbatarwa da alumma wannan yanki da cewa sojojin Nigeriya za su yi iya yinsu don ganin sun kare rayuka da dukiyoyin alummar wannan yanki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here