BARAYIN DAJI MASU DAUKE DA MAKAMAI SUN KOMA YANKIN SABUWA

0
339

BARAYIN DAJI MASU DAUKE DA MAKAMAI SUN KOMA YANKIN SABUWA

@Jaridar Taskar Labarai

Jaridar Taskar Labarai sun samu tabbacin cewa wasu barayin daji masu dauke da muggan makamai suna fashi da garkuwa da mutane sun koma dajin sabuwa daga yankin Batsari da Danmusa da Safana.

Majiya mai tushe ta tabbatar wa da jaridar nan cewa, da yawa sun bar nan yankin sun koma can.

Wannan ya jawo yanzu yankin na karamar hukumar Sabuwa shi ne wanda yafi fama da miyagun hara-hare.
Lissafin da wakilan mu suka tara, a cikin watan nan na Agusta kawai sun kai hare-hare masu yawan gaske, kuma a mafi yawan hare-haren sun yi kisa da garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Jadawalin ya kama kamar haka:
A ranar 24 ga watan Yuli barayin sun je garin Machika sun debi kayan gona sun tafi da wasu mutane daga baya an sako su.

A ranar 7/ 8/2020, sun je kauyen unguwar Dan inna sun tafi da wani mai suna Badamasi.
A ranar 5/8/2020 sunje garin Albasu Ghana sun tafi da mata shidda sune matan Malam shitu 2 da matan Muntari guda biyu, da ‘yan mata guda biyu, diyan Alhaji Abdulhamid da diyar Alhaji Bako.

A ranar 6/8/2020. Sun je garin mararrabar Kondo, gidan Alhaji Ahmad sun yi kokarin tafiya da matarsa aka fafata suka barta suka gudu.

A ranar 9/8/2020, sun shiga garuruwa irinsu unguwar Malam Husaini.

A ranar 10/8/2020 sun je garin Dankurmi da unguwar Sarkin noma, sun tafi har da mutane.

A ranar 12/8/2020 sun sake komawa albasu sun debi kayan gona sun kuma yi garkuwa da mutane.

A ranar 13/2/2020 sunje unguwar mai wasa sun dauki mutane uku, sun yi sata sosai.

A ranar 14/8/2020 sun je garin Rumada, sun tafi da mutane uku.

A ranar 16/8/2020 sun je garin Machika sun yi barna sosai, sun kuma sake komawa garin albasun Ghana, sun tafi da mutum daya, sun kuma kona wani gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here