Shawara ga su Farfesa Umar Ladbo

0
210

Shawara ga su Farfesa Umar Ladbo

Daga Ibrahim Sanyi-Sanyi

Prof Umar Labdo Muhammad, wannan logo get as ebi. Hoton dabino da takobi na nuni ga alakar wannan jami’a da kuke son ginawa a Hadejia da Saudi Arabia. Duk da na lura a baya kuna neman tallafi a hannun yan Nijeriya amma ban sani ba ko gwamnatin KSA ce zata bada kaso mafi tsoka wajen kafa wannan jami’a.

Idan yan Nijeriya ne zasu bada gudunmuwa mafi tsoka, to ya kamata a saka hoton itaciya ko wata dabba dake da mahimmanci ga tarihi ko kuwa tattalin arzikin mu a Arewa maso Yamma. Sannan ya kamata a cire takobi (alamar yaki, tashin hankali ko hukunci) a saka alkalami (alamar ilmi).

Ya kamata kui dogon tunani kafin ku yanke hukunci akan muhimmin abu kamar ‘logo’ sabili dashi sako ne a dunkule ‘that’s subject to human perception and interpretation’.

Da fatan zaku dau shawarwari akan wannan ‘logo’ daga bakin jama’ar gari. Na gode.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here