JAWABIN MANEMA LABARAI; SOJA A AREWA MASO YAMMA NA KARA SAMUN NASARORI AKAN MIYAGU.

0

JAWABIN MANEMA LABARAI; SOJA A AREWA MASO YAMMA NA KARA SAMUN NASARORI AKAN MIYAGU.
Fassarar kanar Aminu iliyasu
Za’a iya tunawa a makon daya gabata, Shalkwatar Operation SAHEL SANITY dake a nan babban sansanin Soja 4 a Faskari ta karbi bakuncin manyan shuwagabanni da suka hada da Chiyamomin Kwamitin Soja na Majalisar Dattijai da ta Wakilan Kasa, Gwamnonin Jihohin Arewa maso Yamma har da na Jihar Neja gami da manyan sarakunan wannan yanki.
A yayin wannan ziyarce ziyarce dai bakin sun bayyana matukar yabonsu ga shugaban Sojojin kasa na Najeriya, Laftanan Janar Tukur Yusufu Buratai tare da Ofisoshi da Sojojin Najeriya kan yunkurinsu na dakile da kuma kawar da ayyukan yan bindiga gami da masu garkuwa da mutane da barayin dabbobi da sauran miyagu inda daga karshe suka hakkanta cewa babu shakka harkokin noma, Kasuwanci da hadahadar jama’a na kara habaka a yankin baki daya.
Duk da wannan dunbin yabo kuwa, dakarun Sojojin basuyi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da ayyukansu. Domin kuwa ko a ranrar 15 August 2020, zaratan Sojojin Operation SAHEL SANITY dake kula da karamar hukumar sabon Birni ta Jihar Sokoto sun samin wata gagarumar nasarar damke wasu dillalan miyagun makamai su uku a shiyyar Dantudu dake Lardin Mailailai a cikin Karamar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto. Mutanen sun hada da Alhaji Adamu Alhassan, Salisu Adamu da Abdullahi Sani. Dukkanninsu yan asalin kasar Niger. Dakarun Sojojin sun sami nasarar datse wadannan masu safarar miyagun makamai ne bisa ga bayanan sirri inda suka samesu da bindigu kirar AK 47 guda 6 tare da gidan harsasai na bindigar AK 47 guda uku gami da alburusai samfirin 7.62 mm Special guda 2, 415, boye a lunguna dabam dabam a cikin motarsu.
Binciken farko ya nuna cewa waddanan miyagun makamai dai na kan hanyarsu tazuwa hannun wasu yan bindiga ne dake a karamar hukunar Isah ta Jihar Sokoto inda amfani da su ka iya jawo halaka ga dubban jama’a da basu jiba basu gani ba.
A cikin wannan yanayi, daya daga cikin masu laifin, Alhaji Adamu Alhassan wanda aka gano cewa yana dauke da cutar suga ya suma wanda kuma ya rasu yayin kokarin gaggauta kaishi asibiti. Duk da haka an ci gaba da binciken sauran abokan illarsa guba biyu domin a bi diddigi wajen kama duk wani mai hannu cikin safarar wannan miyagun makamai. Yunkurin da akeyi tare da hukumomin sirri da na tsaro daga makwabtan kasar nan.
Haka kuma, a ranar 14 August 2020, Sojojin dake kula da shiyyar Kwantaragi sun kame wani mai baiwa yan bindiga bayanai mai suna Tukur Halilu a Kauyen Mutukuda da ke karamar hukumar Maru ta Jihar Zamfara. An same shi da gidajen harsashin bindiga kirar AK 47 guda biyu, da madaukinsu guda day da kuma Paletin Sola guda daya.
Haka nan kuma, a ranar 12 August 2020, dakarun Sojojin sunyi arangama da wasu yan bindiga yayin da suke gudanar da sintiri a cikin karamar hukumar Batsari ta Jihar Katsina inda suka halaka 3 daga cikin yan bindigar suka kuma turmuje sansanonin yan bindiga har guda 12 a wani waje da ake kira Yobe Baranda. Haka zalika a wanan rana Sojojin sunyi nasarar cafke masu baiwa yan bindiga bayanai har su 7 a tsakanin Wenke, Magami da Kasuwar Danjibga dake Jihar Zamfara. Wadannan sun hada da Shehu Abdullahi, Umar Salisu, Abubakar Ahmadu, Mohammed Bashir Tukur, Adamu Tahiyawo, Ibrahim Alhaji Haruna da Mohammed Yusuf.
Yanzu haka dukkanninsu na tsare wajen amsa tambayoyi kafin a mika su hannun hukumar da zata gurfanar da su a gaban Kuliya.


AMINU ILIYASU
Colonel
Nigerian Army Operations Media Coordinator

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here