Yanbindiga sun dauke ‘ya’yan tsohon kwamishina Hudu tare da kashe makwabcinsa a zamfara

0
261

Yanbindiga sun dauke ‘ya’yan tsohon kwamishina Hudu tare da kashe makwabcinsa a zamfara

Wakilinmu Shuaibu Ibrahim Gusau

Da sanyin safiyar yau ne jama’ar garin Gamji dake karamar hukumar Bakura suka wayi gari cikin jimami da tashin hankali, a yayin da suka sami labarin cewa ‘yanbindiga sunyiwa gidan tsohon kwamishinan kana nan hukumomi da masarautu, Alh Bello Dankande Gamji.

Hankan ya fitone ne daga bikin tsohon kwamishinan a lokacin da yakeyiwa abokin aikinmu Karin haske ta wayar tafida gidanka, ya kara da cewa cikin dare misalin karfe hudu iyalinsa dake garin na Gamji suka kira shi suka sanar da shi halin da suke ciki, yace hakan yasa ya dauki mota cikin daren ya Kama hanya.

Ya ce zuwansa ya samu ‘yanbindigan sun harbe wani makwabcinsa mai suna Shafi’u Isa Gamji wanda yayi kokarin kubutar da yaran , Gamji yace sun tafi da yara guda hudu da Mai suna Mujtaba Bello Gamji da Abdulmutallab Bello Gamji sai Kumar Bashiru Gamji sai kuma jami’in taro na farin kaya mai suna, Mansur Suleiman.” inji shi

Hukumar ‘yansanda na jihar zamfara ta bakin jami’in hurda da jama’a, SP Muhammad shehu ya bayyana cewa hukumarsu , ta tabbatar da faruwan Al’amarin Kuma ta rigaya ta tura dakaru da kuma kwararrun jami’an kwastomomi wadanda nan da nan suka fara ayyukan ceto da nufin kubutar da wadanda aka sace tare da kama wadanda suka kashe.

Ya Kara da cewa rundunar tasu ta ba da sanarwa ga tsohon Kwamishina Hon Bello Dankande cewa rundunar tana yin duk mai yiwuwa don ganin an sako wadanda suka sace a gidan kamar yadda aka yi kwanan baya inda aka sace mutane shida (6) wadanda suka hada da shugabannin kananan hukumomin biyu ‘Yan sanda sun kubutar dasu a garin Gizo a Talata Mafara da Bakura LGAs.

Shehu ya Kara da cewa suna kira ga jama’ar gari da su guji fuskantar ‘yan bindiga a yayin wannan mamayar amma su kai rahoton lamarin kan lokaci zuwa‘ yan sanda ko kuma duk wani jami’in tsaro da ke kusa dasu don daukar matakin gaggawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here