ZIYARA ZUWA GONAR SARKIN GONAR KATSINA

0

ZIYARA ZUWA GONAR SARKIN GONAR KATSINA

@Jaridar Taskar Labarai

Garin Maduru na bisa hanyar Daura daga Katsina, mai nisan kilomita ashirin da hudu, daga birnin Katsina. Daga Muduru zuwa kauyen Badole kilomita biyu ne, a nan ne ke da hamshakiyar gonar sarkin noma Mani kuma sarkin gonar Katsina Alhaji Lawal Abdu Muduru.

Matashi ne, wanda ya kawo canji a aikin noma a jihar Katsina, wanda duk Katsina babu manomi daya yanzu kamarsa.

Ya fara noma da yin dami talatin yanzu yana buhunna dubbai, ya fara noma da kansa, yanzu yana da ma aikata sama da dari uku, wadanda ke aiki rani da damina, rani suyi aikin gyaran gona. damina suyi aikin gona.

Ya fara da fili mai taki daidai iyaka, yanzu yana noma sama da hekta Dari uku. Ya fara da takin cikin tiyya yanzu duk shekara tireloli yake saukewa don gonar sa kawai. Ya fara da gonar sa ta Muduru yanzu yana da gonaki a Kankara da Tsanni a karamar hukumar Batagarawa.

Bayan noma sarkin gona na kiwon dabbobi, da tsuntsaye kala-kala. Da ya fara an dauke shi maras wayo yana kai kudi daji,/yanzu an gane ashe shi/ne mai wayon, domin kuwa duk shekara yana cin ribar miliyoyin naira.

Wani abin burgewa da shi, duk harkar shi ta noma akan kanshi yake komai, gwamnati basu taba neman shi ba. Shi kuma bai kai kanshi ba. Ya fada mana cewa, tun da gwamnatin APC ta zo bai taba amfana da komai na aikin nomanshi ba. Ko da kuwa Rabin tiyyar taki ce, balle wata garmar shanu ko iri, uwa uba tarakta.

Yace duk tallafin da ake magana ana yiwa manoma ana bada shi ne, ga ‘yan siyasa ba manoman gaskiya ba.

Yace duk girman noman da muke bamu taba samun ziyara kota karfafa gwaiwa ba, yace yamma da gonata dajin Allah ne, na so in kara girman gonar, na nema ban samu ba. gashinan daji ne, sai ciyawa da hakukuwa ke ta fitowa akai.

Wani canji da ya kawo, dajin da baida wata daraja, yanzu ya zama mafi Albarka. ada anyi tsammanin masara ba tayi, amma a gonar sa ta muduru ana noman dubban buhun nan masara, ana kuma noma gero, wake da gyada.

Sarkin noman Mani kuma sarkin gonar Katsina, yana da mata guda hudu da ya ya guda Goma.

Kusha kallo lafiya na hotunan gonar sarki Alhaji Lawal Abdu Muduru karamar hukumar Mani jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here