ANA CI GABA DA KAI HARI A SABUWA

0

ANA CI GABA DA KAI HARI A SABUWA
muazu hassan
@ taskar labarai
Barayin daji masu fashi da garkuwa da mutane da yanzu suka mai da karfinsu a karamar hukumar sabuwa ta kudancin jahar katsina.suna cigaba da kai Hari ba yankewa.
A ranar 18/8/2020 sun kai hari a garin dungun muazu.sun kwashi abinci har da dafaffe.kuma ana tsammanin sun tafi da wasu mutanen.
A kuma ranar suka wuce garin sayau mai kasuwa .nan sun harbi mutane biyu sun kwashi dabbobi da kayan abinci.har da kayan kwanciya.
Yanzu a duk fadin jahar katsina, karamar hukumar sabuwa ce, kawai lamarin ba sauki.a kowace Rana akwai kauyen da aka kaima Hari.
Yankunan Batsari, jibia, safana, dutsin ma da Dan Musa duk abin ya ragu sosai.sai abin da ba a rasa ba. Wanda ake danganta nasarar da amsar addu a .wadda jama a keyi ba dare ba Rana.
Jaridun taskar labarai sun dau mutane biyu aiki a yanki don rika kawo abin dake faruwa da dumi dumi duminshi.zasu sa ido a sabuwa, faskari da Dandume.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here