Karamin Ministan Ilimi, Nwajiuba, Ne Zabi Nagari, Cewar Wata Kungiya

0

2023: Karamin Ministan Ilimi, Nwajiuba, Ne Zabi Nagari, Cewar Wata Kungiya

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

Wata kungiya mai suna Project Nigeria Group ta bayyana ra’ayinta da cewa, Karamin Ministan Ilimi na Nijeriya, Hon. Chukwuemeka Nwajiuba, shi ne ya fi dacewa da ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023 da ke tafe, ta na mai cewa, ministan shi ne zabi nagari ga ’yan daukacin Nijeriya.

Sakataren kungiyar, Kwamred Chinedu Ogubuke (KSM), shi ne ya bayyana matsayar kungiyar bayan kammala ganawarsu da sauran shugabannin kungiyar, wadanda su ka hada da Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi, Shugaban kungiyar na Kasa bakidaya, wanda ya fito daga Jihar Kano, da Rt. Hon. Nkem Abonta, Shugabanta na yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya.

Everything on JUMIA

A sanarwar da ya raba wa manema labarai a Abuja ranar Larabar da ta gabata, kungiyar ta ce, “kamar yadda dukkan ‘yan siyasa su ka sani, Mai Girma Hon. Chukwuemeka Nwajiuba, wanda magoya bayansa ke yi wa kirari da Magajin Mai Gaskiya, ya yi magana da Shugaban Kasa, don ya bai wa al’ummar yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya dama su ma su shiga cikin takarar shugabancin kasa a 2023, saboda ganin cewa tun shekara ta 1999 su ke neman wannan damar, amma ba su samu ba.

“Mutanen Kudu maso Gabashin Nijeriya na yawaita korafin cewa, ba a tafiya da su a takarar da a ke yi na kasar nan alhali su na daya daga cikin manyan kabilu da mu ke da su a kasa bakidaya.

“Kasancewar Hon. Nwajiuba (Magajin Mai Gaskiya) na daya daga cikin fitattun ’yan siyasa da a ke da su a Kudu maso Gabas, wanda kuma za a iya bayyana shi a matsayin daya daga cikin amintattun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa ya yanke shawarar yin takarar shugabancin kasar nan shekara ta 2023 idan Allah ya kai mu.

“Sakamakon haka, Hon. Nwajiuba, a na hasashen bayan shawara da Shugaban Kasa da ya yi, ya fara tsara yadda zai tafiyar da siyasarsa yayin da magoya bayansa su ka dukufa wajen nuna ma sa goyan bayansu ta fannin kirkiro kungiyoyi daban-daban daga lunguna da kuma sakuna da ke fadin kasa.

“Matasa sun nuna farin cikinsu, don ganin matashi dan uwansu ya fito, don ya gyara kasar nan ta hanyar kawo cigaba ta fannoni daban-daban ga mutanen Nijeriya da kuma ita kanta Nijeriya din.”

Sanarwar ta cigaba da cewa, daya daga cikin kungiyoyin magoya bayansa su ne Project Niger Group (PNG), wacce ke da rassa a jihohi 36 da ke fadin kasar.

Rahotanni sun nuna cewa, manyan ’yan siyasa da ke Kudu maso Gabas sun ziyarci Hon. Nwajiuba, don nuna son ya fito neman shugabancin kasar 2023.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa, “sun nemi ya fito ne, don ganin cewa za su iya kai labari, saboda shekara ta 2023 lokaci ne na ‘Yan Kudu maso Gabas. Sannan kuma su na ganin zai iya lashe zaben fiye da kowane Dan Kudu maso Gabas, don ganin shi yardajje kuma makusanci ne ga Shugaba Buhari.

Za mu iya tuna cewa, Hon. Nwajiuba (Magajin Mai Gaskiya) ya taba neman takarar kujerar shugabancin jiharsa ta Imo a karkashin jam’iyyar ANPP a 2003, wacce ya lashe zaben fidda gwani ya zama dan takarar jam’iyyar yayin da a lokacin Shugaba Buhari ne dan takarar shugabancin kasar a jam’iyyar.

Haka kuma shi din dai Hon. Nwajiuba ya sake zama dan takarar gwamnan jiharsa a karkashin jam’iyyar CPC a shekara ta 2011 yayin da har ila yau Shugaba Buhari ke takarar shugabancin kasar a jam’iyyar a wancan lokacin.

Bugu da kari, Hon. Nwajiuba na daya daga cikin mutanen da a ka zaba a kwamitin mutane uku da su ka yi gwagwarmaya, sannan su ka kai ruwa rana, don ganin cewa, CPC da kuma ACN sun sauke tutarsu, winda a sanadiyyar haka ne a ka yi hadaka (Maja) a ka kirkiro jam’iyya mai mulki a yanzu, wato APC.

Wasu daga cikin shugabannin tafiyar Nwajiuba ta neman shugabancin Nijeriya a 2023 sun hada da Alhaji Yusuf Sulaiman, Shugaban Arewa maso Yamma; Rt. Hon. Abdullahi Ibrahim Halims, Daraktan Tuntuba; Hon. John Eyegh, Shugabancin Jihar Benuwe; yayin da Hon. Yusuf Ahmed Tijjani ke shugabancin Jihar Kogi.

Saura sun hada da Abdulhakeem Abdullahi, wanda ke shugabancin Jihar Neja, yayin da Usman Hassan ke shugabancin Birnin Tarayya Abuja da kuma da dama, wadanda ke shugabantar sauran jihohi.

Har kawo zuwa hada wannan rahoto dai, Karamin Minista Nwajiuba bai fito karara ya bayyana wa jama’a niyyarsa ta fitowa takarar shugabancin kasar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here