Hukumar ta ce fina-finan Kano ba ta da hurumin tace waƙoƙi–Aminu Ala

0
405

Hukumar ta ce fina-finan Kano ba ta da hurumin tace waƙoƙi–Aminu Ala

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Fitaccen mawakin Hausa, Aminu Abubakar Ala wanda aka fi sani da Alan waka, ya ce hukumar tace fina-finan jihar Kano ba ta da hurumin tace waƙoƙin yabon Annabi.

Aminu Ala ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa ta kafar shafinta na Instagram,
Ala ya ce “yin haka daidai ya ke da tsuke tinanin mawakan saboda ita wata baa ta ce ta”

In dai baa manta ba kwanakin baya hukumar tace fina-fanai ta Kano ta ce babu wani sha’iri da zai ƙara fitar da waƙa a jihar, sai an tantance shi kuma an ba shi izini,

A makon da ya gabata ma dai Shairai mata sun kai wa shugaban wannan hukuma Ismail Na’Abba Afakallah ziyarar ban girma dangane da yunkurinsa na yin garanbawul ga harkon yabo a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here