MAHARAN DAN MUSA DAGA SHINKAFI SUKA ZO

0

MAHARAN DAN MUSA DAGA SHINKAFI SUKA ZO

Mahmood Ahmad
@ taskar labarai

A daren ranar laraba wasu mutane dauke da makamai suka kai hari a garin Danmusa karamar hukumar Danmusa jihar Katsina. Mutane sun shiga garin Danmusa wajen karfe sha daya na dare suka yi ta harbi ba kakkaftawa duk suka tada hankalin kowa a garin sannan suka sulale, ba tare da an kama ko kashe wani ba daga cikin su.

Binciken Taskar Labarai ya gano cewa, maharan sun taso ne daga dajin shinkafi cikin jihar zamfara majiyarmu tace, sun baro dajin tun karfe hudu na yamma kamar yadda mutanen kauyukan yankin suka tabbatar mana.

Daga shinkafi sun yanko suka zo dajin dumburun duk a cikin Zamfara. Suka shigo zuwa wata daba da ake kira Gora, suka ratso ta Guzurawa, da Gimi. Ko ina suka yadda zango suna kara yawa.

Majiyarmu tace, niyyarsu su kai ma sojan dake da sansani a Marar Zamfarawa dake Danmusa hari.

Majiyarmu tace sun yada zango wani waje, bayan shaida masu halin da wannan sansanin sojan yake sai suka canza shawara suka shiga garin Danmusa suka yi harbe-harbe, suka gudu.

Majiyarmu tace, maharan ba suyi kama da zallar Fulani masu dauke da makamai ba, a a sun fi kama da mayaka wadanda ke neman wani abu ko kuma sun fito don kara horo.

Duk kauyuka da garuruwa dake tsakanin Shinkafi zuwa Dumburun da suka ratsa zuwa hanyar Marar Zamfarawa sun ga wucewarsu, basa cewa kowa komai.

Majiyarmu tace ana tsammanin sansanin sojan dake garin Marar Zamfarawa suka so kai ma hari ko dai don su kwashi makamai ko suyi kisa, kila da suka lura in suka kai harin babu nasara suka fasa.

Maijiyarmu tace, da ada ne lokacin da kwamitocin zaman lafiya ke aiki, da tun daga daji za a iya sanarwar na cikin gari su kuma sanarwa jami’an tsaro.

Amma da yake an rusa wadancan kwamitocin, tun da yamma aka san maharan suna dajin Jibia da Batsari zasu wuce, har suka shiga Safana ba wanda zasu fada mawa.

Wani ya bada shawarar ya kamata gwamnati ta farfado da kwamitin nan na kananan hukumomi ko domin musayar bayanai.
________________________________________________
Taskar labarai na bisa yanar gizo akan www.taskarlabarai.com da ta turancinta mai suna the links news dake akan www.thelinksnews.com duk sakon akan 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here