Shugaba Buhari ya nada Amokachi Mataimaki a harkokin Wasanni

0

Shugaba Buhari ya nada Amokachi Mataimaki a harkokin Wasanni

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada fitaccen dan wasan kwallon kafa ta Nigeriya, tsohon dan wasan Super Eagles Daniel Amokachi a matsayin Mataimakin na Musamman kan harkokin Wasanni,

A wata wasika da aka rabawa manema da ta samu sa sannun Sakataren gwamnatin Nigeriya Mista Boss Mustapha nadin da aka bayyaya a ranar 17 ga watan Agusta 2020, ya ce“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa, Shugaban Jamhuriyar Tarayyar Najeriya ya amince da nadin Mataimaki na Musamman kan Wasanni.

Nadin ya fara aiki ne daga 11 ga watan Agusta, 2020. ”

Tsohon dan wasan Everton da ke Ingila a farkon shekarar 2020 an nada shi a matsayin jakadan kwallon kafa ta Najeriya.

Amokachi ya fara aiki ne a Kaduna tare da kungiyar kwallon kafa ta Ranchers Bees ta Kaduna, ya buga wa Club Brugge ta Belgium, Besiktas ta Turkiyya, Everton na Ingila da Colorado Rapids.

Ya taka leda a wasannin cin Kofin Duniya uku, ya lashe Kofin Kasashe Afrika biyu a matsayin dan wasa da Mataimakin Koci, ga Stephen Keshi, Austin Eguavoen, Samson Siasia da Lars Largerback. Ya lashe zinare a gasar kwallon kafa ta Atlanta 1996.

Yawan rauni da ya dinga samu a kafa ne musabbabin ja bayansa a kwallon kafa inda ya yi ritaya da buga tamula.

ya horar da kungiyar ‘yan kasa da shekaru 23, sannan ya zama Mataimakin Kocin Super Eagles da kuma horar da Nasarrawa United.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here