MATAN DA KE GASA GURASA A KANO SUN YI BARAZANAR YAJIN AIKI

0

MATAN DA KE GASA GURASA A KANO SUN YI BARAZANAR YAJIN AIKI

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Matan da ke gudanar da sana’ar sai da gurasa a juhar Kano sun ce, za su tsunduma yajin aikin gashin gurasar biyo bayan tashin gwauron zabi da fulawa da kuma sauran kayan aikin yin gurasar su ka yi a Kasuwanni.

Wasu daga cikin matan da ke sana’ar sun bayyana haka ne a tattaunawar da suka yi da manema labarai a birnin Kano.

Da ta ke jabawabi Hajiya Amina Aikawa wadda ita ce shugabar ƙungiyar masu sana’ar gashin Gurasar ta ce, kafin azumin da ya gabata ana sayar da buhun Fulawa akan naira 9,200 amma yanzu buhun ya kai naira 14,000.

Ta kara da cewa, sauran kayan haɗin gurasar ma sun yi irin wannan tashin gwauron zabi da hakan ya sanya su ke fuskantar matsala tsakaninsu da ƴan talla saboda sun yi niyyar yi wa gurasar ƙarin kuɗi amma ƴan tallar suka ƙi amincewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here