MIJI YA KULLE MATARSA MAI CIKI A DAKI HAR TA MUTU A KANO

0

MIJI YA KULLE MATARSA MAI CIKI A DAKI HAR TA MUTU A KANO

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Jami’an ‘yan sanda a jihar Kano sun tabbatar da gano gawar wata mata da ake zargin mijin ta ya kulleta a cikin ɗaki har ta yi kwanaki 3 da mutuwa.

Jaridar turanci ta Internet Prime Time News ta ruwaito cewa, Lamarin ya faru ne a unguwar Mariri da ke yankin ƙaramar hukumar Kumbotso.

Rahotonni sun bayyana cewa an gano gawar matar har ta kumbura kuma ta fara yin wari wanda hakan ce ta sanya makobtan marigayiyar suka fara jin warin har suka sanar da jami’an ‘yan sanda.

Hakan yasa mazauna unguwar suka kira ‘yan sanda kuma tuni suka kama mijin nata mai suna Auwalu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce suna cigaba da binciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here