SABBIN HARE HARE A FASKARI DA SABUWA

0

SABBIN HARE HARE A FASKARI DA SABUWA
Muazu hassan
@ taskar labarai
Miyagu masu dauke da makamai suna ci gaba da kai hare hare kananan hukumomin sabuwa da faskari. Jaridar taskar labarai ta tabbatar cewa a satin da muke a ciki sun kai hare hare kamar haka.
A ranar laraba, 20/8/2020 maharan sun kai farmaki garin Maigora ta karamar hukumar faskari.inda ake zargin sun tafi da mutane biyu.
A ranar jumma a 21/8/2020. Maharan sunje gari Dan takari a karamar hukumar Dandume ana tsammanin wata mata ta rasu saboda firgita, wasu mutane shidda kuma sun bace ba a gansu ba.
A daren asabar 22/2/2020 maharan sunje dungun mua zu a karamar hukumar sabuwa, sun tafi da mutane uku.suka sako dattijo daya da suka lura baya da lafiya.
Jaridar nan na da wakilan musamman a yankin don kawo rahoton tsaro a yankin.duk wani kyankyashen bayani ana iya aikawa da sakon haka ga lamba 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here