YAN ASALIN KATSINA DAKE RIKE DA MUKAMIN A TARAYYA SUN KAWO TALLAFI GA YAN GUDUN HIJIRA

0

YAN ASALIN KATSINA DAKE RIKE DA MUKAMIN A TARAYYA SUN KAWO TALLAFI GA YAN GUDUN HIJIRA
========================================

“A yau Asabar 22/08/2020 yan asalin Jihar Katsina masu rike da mukamai matakin Gwamnatin Tarayya sun bada tallafi ga yan Gudun Hijra na karamar hukumar Faskari da Batsari da rikicin yan bindiga Barayin Shanu ya shafa”.

MASU RIKE DA MUKAMAN DA SUKA BADA TALLAFIN SUN HADA DA…..!

(1) MD FERMA. Engr. Nuraddeen Rafindadi Shugaban hukumar kulada gyaran hanyoyi ta Kasa.

(2) MD. (FMBN) Arc. Ahmed Musa Dangiwa Shugaban Bankin bada lamuni ga ma’aikata na kasa.

(3) DG. SMEDAN _ Dr. Dikko Umar Radda Shugaban hukumar bada tallafi ga masu kananan Sana’o’i da matsakaita ta kasa.

(4) DG. NIA, Alh. Ahmed Rufa’i Abubakar Kofar Durbi Katsina, Shugaban hukumar kulada leken asirin na kasa. (NIA).

(5) MD. (NSPMC) _ Alh. Abbas Umar Masanawa Shugaban Kamfanin dake sanya ido kan yadda ake buga kudi na kasa.

(6) MD. NEXIM BANK na kasa Alh. Abba Bello Shugaban Bankin (NEXIM) na kasa.

(7) DG. (FRCN) Dr. Mansur Liman Shugaban gidan rediyo na Tarayya.

(8) MD. NIGERIAN PORT AUTHORITY _ Haj. Hadiza Bala Usman shugaban hukumar kulada zirga, zirgar jiragen ruwa ta NIGERIA.

(9) DG. NIGERIAN METREO LOGICAL (NIMET) Prof. Sani Abubakar Mashi shugaban hukumar (NIMET) ta kasa.

“KAYAN TALLAFIN DA SUKA BADA SUN HADA DA”.

(1) Kayan yara dozin (90) kowane dozin yana da guda (12) ya kama bandir (36) za’a rabasu ga yara (1080).

(2) Atamfa leda (200) kowace leda tana dauke da atamfa (10) ya kama bandir (20) za’a rabasu ga mace (2000).

(3) Shaddoji Bandir (25) yadi biyar, biyar za’a rabasu ga mutum (1500).

(4) Man shafawa (VASELINE) Katan (84) kowane katan yana dauke da man shafawa (24) za’a rabasu ga mutum (2000).

(5) Sabulun wanka (OLIVE) Katan (28) mai dauke da Sabulun wanka guda (72) za’a rabasu ga mutum (2000).

(6) Sabulun wanki Katan (20) mai dauke da Sabulun wanki (100) katan (20) za’a rabasu ga mutum (2000).

“KARAMAR HUKUMAR FASKARI”.

“Ta samu kayan yara dozin (60) wanda za’a rabasu ga yara (720), Atamfa Leda (133) za’a rabasu ga mata (1,330), shaddoji bandir (16) mai yafi (60) za’a rabasu ga mutum (972), Man shafawa VASELINE katan (56) za’a rabasu ga mutum (1,344), Sabulun wanka katan (19) za’a rabasu ga mutum (1,296), Sabulun wanki Katan (13) mai dauke sabulu guda (100) za’a rabasu ga mutum (1,300)”. Karamar Hukumar Faskari ta samu kishi biyu bisa uku na kayan saboda matsalar tsaron tafi shafar ta”.

KARAMAR HUKUMAR BATSARI.

“Ta samu kayan yara dozin (30) za’a rabasu ga yara (360), Atamfa Leda (67) za’a rabasu ga mata (670), shadda bandir (8) mai yadi (40) za’a rabasu ga mutum (488), Man shafawa VASELINE katan (28) za’a rabasu ga mutum (672), Sabulun wanka katan (9) za’a rabasu ga mutum (648), Sabulun wanki Katan (7) mai dauke da guda (100) za’a rabasu ga mutum (700)”.

See also  Ɗalibai biyu sun rasa ransu a sakamakon harbi da bindiga a garin Katsina

“Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari shine Babban bako na musamman wajen taron bada kayan tallafin, kuma shine ya kaddamar da bada kayan tallafin ga yan Gudun Hijrar na karamar hukumar Faskari da Batsari. An kaddamar da bada kayan tallafin a sakatariyal karamar hukumar Faskari”.

“Da yake gabatar da jawabi Amadadin yan asalin Jihar Katsina masu rike da mukamai matakin Gwamnatin Tarayya, Arc. Ahmed Musa Dangiwa “ya bayyana cewa sun hadu sun bada wannan tallafi matsayin su na yan asalin Jihar Katsina da shugaban kasa M. Buhari yaba mukamai”.

“Arc. Dangiwa “ya yaba ma Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari wajen kokarin shi na magance matsalar tsaro daya addabi Jihar Katsina duk yanayin tattalin arzikin da kasar nan take ciki”. “Daga karshe yayi addu’a Allah ya kawo mana karshen wannan masifa da muka samu kanmu ta matsalar tsaro a Jihar Katsina da kasa baki daya”.

“A nashi jawabin Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari “ya godema masu rike da mukaman matakin Gwamnatin Tarayya. “Gwamnan “ya cigaba da cewa basu bada wannan tallafi ba, saida sukayi shawara dashi zasu bada tallafi ga yan Gudun Hijra”. Gwamnan “ya cigaba da bayyana “cewa, abinda yake muhimmi garemu, Al’umma su koma garuruwan su da gidajen su, su cigaba da gudanar da harkokin rayuwar su cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali kamar yadda suka saba”.

“Jami’an tsaro ba zamu tabbatar da an samu zaman lafiya ba, sai Al’umma sun koma garuruwan su da gidajen su, kuma sun cigaba da gudanar da harkokin rayuwar su cikin natsuwa ba tareda wata barazanar tsaro ba”. “Kuma shine zamu tabbatar da kwalliya ta biya kudin sabulu. “Daga karshe Gwamnan ya jawo hankalin Al’umma da kowa ya zama Dan sandan kanshi don taimaka ma harkar samar da tsaro a cikin Jihar nan”.

“Bada tallafin ya samu Halartar mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Qs. Mannir Yakubu, yan majalisar zartarwa da yan majalisar Dokoki ta Jihar Katsina, daga cikin su, akwai Kwamishinan ma’aikatar kulada harkokin wasanni walwala dajin dadin jama’a, kuma shugaban komitin kulada yan Gudun Hijra na Gwamnatin Jihar Katsina Hon. Sani Aliyu Danlami, Mataimakin kakakin majalisar Dokoki ta Jihar Katsina wanda shine yake wakiltar karamar hukumar Faskari a majalisar Dokoki ta Jihar Katsina Hon. Shehu Dalhatu Tafoki, Hakimin Faskari dana Mai Ruwa”. Dadai sauransu”.

Rahoto.
Surajo Yandaki
Directer Editing
Mobile Media Crew
22/08/2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here