ALHAJI SALISU MAMMAN CONTINENTAL: FARIN WATA HASKA GARI

0

ALHAJI SALISU MAMMAN CONTINENTAL: FARIN WATA HASKA GARI
Abdurrahaman Aliyu
@ taskar labarai

Alhaji Salisu Mamman (Continental) dan kasuwa ne mai zaman kansa da ya kafa tarihin da shekaru dubu nan gaba ba za a manta da shi ba.

Gidauniyar sa ta ‘Continental’ yanzu a jihar Katsina babu wata gidauniya da ta talafi al’umma kamarta, ko shakka babu Alhaji Salisu bango ne abun jingina ga talkawa da sauran masu karamin karfi a fadin jihar Katsina baki daya.

Tarihi ba zai taba shudewa ba ko kuma ya manta ranar 15/8/2020 wadda ita ce ranar da ta zama mabudi ko kuma dan ba ga al’ummar karamar hukumar Rimi ta fuskar ingantuwar tattalin arziki da kuma bunkasuwa da cigaban daliban karamar hukumar. A ranar ne Alhaji Salisu Mamman ya bayar da tallafin jari ga mata masu kananan sana’o’i dubu daya (1000) da kuma dalibai sama dari bakwai (700+) inda kowanen su ya samu tallafin naira dubu goma (10,000) wanda in ka tara kudin za su zama sama da naira miliyan 17.

A dai wannan ranar ne mai girma gwamnan jihar Katsina Rt. Hon Aminu Bello Masar da mataimakinsa QS. Manni Yakubu da sauran masu ruwa da tsaki suka kuma sanya harsashen ginin dakin taro na dalibai wanda wannan bango kuma jigo Alhaji Salisu Mamman ke ginawa a makarantar sakandire ta Al’umma da ke Kadandani, wanda dama can shi ne ya assasa wannan makaranta.

Bayan wannan gagarumin aiki kuma sai tarihi ya kara maimaita kansa a ranar 22/8/2020 inda Alhaji Salisu ya tara kafutanin Katsinawa wajen bude katafaren ginin mazaunin dindin na kamfaninsa da zai bayar da ayyukan yi ga al’ummar jihar Katsina sama da dubu goma (10,000+) tare kuma da kaddamar da ginin dakin kwantar da marasa lafiya mai daukar gado ashirin da hudu (24) a babbar asibitin jihar Katsina, wanda gini ne da yake kyauta kuma sadukarwa ga talakawan jihar Katsina.

Wannan gagarumin taro ya samu halartar masu ruwa da tsaki a gwamnatin jihar Katsina wadanda suka hada da mai girma gwamnan jihar Katsina Rt. Hon Aminu Bello Masar, da mataimakinsa QS Mannir Yakubu da Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da Alhaji Sanusi Gidado shugaban rukunin bankunan Kasuwanci na shiyar Arewa maso yamma da Kauran Katsina Hakimin Rimi Alhaji Nuhu Abdulkadir da kwamishinoni da masu rike da madafun iko na ciki da wajen jihar Katsina.

A bangaren ‘yan kasuwa kuma akwai shahararren dan kasuwar nan Alhaji Dahiru Bara’u Manga da sauran giggan ‘yan kasuwar ciki da wajen jihar Katsina.

A duka tarukan Mambobin wannan gidauniya sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin wadanann taruka sun samu nasara wadda zata zama abun kwatance a jihar Katsina, mambobin sun hada Alhaji Sani Umar Kadandani da Eng. Surajo Yazid Abukur MD KASROMA da Hon. Mu’azu Lemamu Tsagero da Hon. Nasiru Ala Iyatawa da Hon Bilyaminu Muhammad Rimi da Hon. Abdurahman Kurabau da sauransu.

Ko shakka babu Alhaji Salisu Mamman Continental Bango ne abun jinginar talakawa kuma farin wata ne mai haska gari, sanan tsani ne matakar bayi. Irin wadannan ayyukan alheri da ya shimfida a jihar Katsina wani tarihi ne ya kafa wanda shekaru da dama ba zai gogu ba a jihar Katsina da ma duniya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here