Anyi kira da a tallafawa Mata da matasa da Yara dan ci gabanta rayuwansu .

0

Anyi kira da a tallafawa Mata da matasa da Yara dan ci gabanta rayuwansu .

Shu’aibu Ibrahim daga Gusau

Maimartaba Sarkin zamfaran Anka, Alh Attahiru Ahmad Muhammad, kuma shugaban majalidar sarakuna na jihar zamfara, ya yi kira ga masu tsara manufofi tun daga matakin kananan hukumomi da jihohi da kuma tarayya da su fito da manufofin da za su tabbatar da ci gaban matasa don karfafawa juna da kuma kyakkyawan rayuwar su a kasan nan.

Sarkin ya yi wannan kiran ne yayin zantawarsa da manema labarai a Gusau, jihar Zamfara ranar Lahadin da ya gabata, ya bukaci masu tsara manufofin da su fito da tsare-tsare da shirye-shirye wadanda zasu tabbatar da yancin mata da yara, ya ce Samar da irin wadannan manufofin sun zama tilas saboda bukatar ilimantar da mata akan irin wadannan hakkoki.

Sarkin ya kara da cewa galibin matan Arewa, basu jahilcin ‘yan uwansu maza ba ,yace mata da yawa sun bayyana cewa addinin Islama ne ya bai wa namiji damar ya auri mace fiye da daya, kuma ya ba shi umarnin zama shugaban iyali don tabbatar da adalci a tsakanin su da yayansu.

See also  DIKKO RADDA ZAI KAMMALA DAM ƊIN ƊANJA 

Alh Attahiru yace ya yi takaicin cewa wasu daga cikin matan na cutar da su mazajen ,da kuma wasu daga cikin mazajen matan da ke azabtar da su ta hanyar lalata ,ko mutuwar aure da wasu dalilai da ke sa uwayensu ba sa zama tare .

Sarkin ya jaddada cewa yakamata a kirkiro wani taron masana da na ilimi mai ma’ana , tare da kudurin haduwa a duk shekara tare da kawo mafita don magance matasa da mata da yara tare da fadakarwa tare da kokarin magance rikicin cikin gida da sauran laifuka. hade da matasa da mata.

Ya kara da cewa “Wannan ma zai yi matukar amfani wajen hada matan su da surukan su da kuma magance matsalolin da matan su ke hana mazajensu ta hanyar taimakawa dangin sa wanda hakan ke haifar da dumbin matsaloki ” .Ya ce

Ya ce taron a cewar sa zai iya buga littafi wanda zai iya kasancewa a cikin girma ko a sabunta shi kowace shekara kuma zai iya kasan cewa ga kowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here