Gwamnatin Kano ta dauki Alarammomi 60 aiki don karantar da Almajirai
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da ɗaukar alarammomi 60 aiki a faɗin jihar Kano don su koyar a makarantun Allo na zamani guda 15 da ke jihar.
Bayanin haka ya fito ne ta bakin kwamishinan Ilimi na jihar Kano, Sanusi Ƙiru, fitar ranar Talata ya ce wannan ɗaukar aiki zai fara aiki ne nan take.
Ya ce gwamna Ganduje ya bayar da izinin ɗaukar malaman ne biyo bayan buƙatar haka da hukumar kula da makarantun ƙur’ani da na Islamiyya ta Jihar Kano, KSQISMB, ta gabatar ranar Litinin.
“Wannan ɗaukar aiki ya ƙara nuna jajircewar Gwamnan wajen kakkaɓe barace-barace da kuma yadda ake kafa Makarantun Ƙur’ani a jihar Kano ba tare da samar da abubuwan buƙata na dole ba.
“Waɗannan abubuwa su ne kamar banɗakuna, ɗakunan girki da kuma manhaja ta bai ɗaya wadda za ta sa almajiran su haddace Kur’ani Mai Tsarki, su kuma samu ilimin boko a mahalli mai tsafta da tsaro”, in ji shi.
Sanusi Ƙiru ya kara da cewa za a tura alarammomin 60 zuwa sabbin makarantun kwana na almajirai da aka gina a ƙananan hukumomin Bunkure, Madobi da Ɓagwai.
Sannan ya ce waɗannan sabbin makarantu ƙari ne a kan guda 12 da ake da su tuntuni a jihar.