Operation SAHEL SANITY sun yi nasarar kama manyan motoci guda 7 dauke da shanu

0

Operation SAHEL SANITY sun yi nasarar kama manyan motoci guda 7 dauke da shanu

Shu’aibu Ibrahim Gusau

An bayyana cewa a tsakanin ranakun 19 – 20 ga watan Augusta 2020, Sojojin Operation SAHEL SANITY sun yi nasarar kama manyan motoci guda 7 dauke da shanu da ake zargin cewa na sata ne a kan hanyar Jibia zuwa Katsina da kuma hanyar Gusau zuwa Zaria.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin jami’in hulda da kafafen yada labarai na rundunar sojan Nageriya, kanal Aminu Iliyasu, a lokacin da yake yiwa manema labarai bayani a Faskari jihar katsina.

Iliyasu ya bayyana cewa tuni dai an mika su zuwa hannun Hukumar yan Sanda ta Jihar Katsina da kuma Kungiyar Karbar Kwatattun Shanu ta Jihar Zamfara.

Ya ce dukkanin mutanen da aka kama dai na ci gaba da amsa tambayoyi kafin a mika su hannun hukumar da zata gurfar dasu a gaban kuliya.

Kanal Aminu ya bayyana cewa a ranar 21 ga watan Augusta kuwa, Sojojin sun yi anfani da bayanan sirri inda suka afkawa wata maboyar yan bindiga dadi a kauyen Dogon Karfe dake cikin karamar hukumar Bakura ta Jihar Zamfara inda suka sami bindigogi kirar gida guda hudu gami da gidan harsasai dake cike da harsasai a wani kufai.

Ya kara da cewa dadin dadawa, a wannan rana kuma Sojojin dake kula da shiyyar Wagini sun sami nasarar cafke wani kasurgumin dan bindiga dadi mai suna Isuhu Ibrahim wanda akeyiwa lakani da Bula wanda suka dade suna addabar mutanen yankin tare da abokanen ta’asarsa.

See also  Yan Sanda Jahar Katsina ta kama Mutane 1,102 da ake zargi da aikata laifuka a jihar a shekarar 2022.

Haka zalika, a ranar 20 ga watan Augusta 2020, Sojojin Operation SAHEL SANITY masu kula da Daki Takwas sun kaddamar da wani binciken motoci na ba zato inda suka yi nasarar kame wata mota kirar Toyota Corolla mai lambar rigista DAL 41MT. Sojojin sun gano bindigogi sababbi kirar gida guda 11 tare da harsasai guda 150 da aka boye a sako daban – daban na motar.

Ya ce an dai kame mutanen su biyar dake tafe a cikin motar inda binciken farko ya nuna cewa wadannan miyagun makamai dai na kan hanyarsu ne ta zuwa Kofar Dinya a karamar hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara gabanin kame su.

Ya Kara da cewa a wani mai kama da Wannan a cigaba da gudanar da yaki da ‘yanbindigan a ranar 23 ga watan Augusta 2020, Sojoji sun gudanar da wani samame a wata barauniyar mahakar maadanai a wani guri da aka sani da suna Gadan Zaima a cikin karamar hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara. A yayin wannan samame, dakarun sun yi nasarar kame mutum 150 yayin da kuma suka bindige daya daga cikin su lokacin daya ranta a na kare.

Ya ce Sojojin sun sami nasarar kwato bindigogi kirar gida har guda ashirin daga hannun masu laifin,binciken farko ya nuna cewa irin wannan ayyukan barayin ma’adanai dai shine ake amfani da shi wajen hura wutar ayyukan yan bindiga dadi a wannan yanki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here