Fitaccen jarumin barkwanci a fina-finan Hausa na Kannywood, Musa Mai Sana’a, ya ce yana matukar nadama a game da tsinewa ko la’antar kansa da yake yi a cikin wasu fina-finan da ya fito.
A cikin wata tattaunawa da BBC ta Instagram, Mai Sana’a ya ce a da ya yi hakan saboda rashin kwarewa.
Amma a hankali- a hankali sai ya fahimci cewa wannan abu da ya ke fa ba abune mai kyau ba.
Ya ce “Da farko-farkon fina-finai na na yi ta yin abubuwa wadanda ni a ganina dai-dai ne, amma daga bisani bayan da wasu mutane suka ja hankalina a kan abubuwan musamman zagi ko tsinewa kaina da nake, sai na fahimci cewa lallai yakamata na daina”.
Mun Ciro daga shafin Sarauniya na Facebook