MATSALAR YUNWA DA TSADAR RAYUWA YA KAMATA MU FADAWA JUNA GASKIYA.
Daga Muazu Umar Hardawa Bauchi.
Halin da muke ciki na tsadar rayuwa da talauci wasu na ganin babu laifi daga shugabanni Allah ne ya kawo har suna danganta lamarin da cewa lokacin annabi anyi irin wannan wahala, alhali wancan lokaci kowa ya sani annabi da sahabbai basa ci sai kowa ya ci.
Kuma annabi ya ce kowane shugaba zai zo daure ranar lahira adalci da yayi wa talakawa shine zai kunce shi, idan har mun yarda da wannan hadisi mu danganta shi da wannan lokaci da sanata daya ke karbar.milyan 30 albashi a wata daya kudin kusan farfesa 50 da ke koyarwa a jamia.
Sanin kowane lokacin annabi saw babu rufe boda saiko a samu fari ko talauci da raahi,a tafi sham a tafi madina ko habasha kasuwanci halas ne. Amma yanzu ance yin kasuwanci haramne da wata kasa kowa yayi noma ya cida bakinsa alhali ba kudin nomar ba abinda za a ci ayi nomar wani wajen ba filin nomar me ake nufi kenan.
Don haka yanzu kowa ya sani gangancine kowa ya rufe kasarsa babu abinci yasan dole Wanda ya saya ya tara yayi rashin tausayin talakawa. Bayan haka Kuma dole a samu rashin tsaro da aikata miyagun ayyuka don ciyar da kai. Saboda idan wani ya rage buri ya nema daga halas ko ya kwana da yunwa wasu zasu shiga aikata laifi musamman matasa da Yan mata da zawarawa don neman abin da za su cida bakinsu.
Ko rantsuwa na Yi nasan bazan yi kaffara ba, nasan kudin da ake kashewa wajen gyara tarbiyya da yaki da ya taadda wadanda rufe kan iyaka ya karya su, ribar nomar shinkafa ba zata cike gurbin kudin da ake kashewa wajen sayen makamai da kayan aiki don seta mutane ba.
Baa maganar rai da dukiyar da ake rabawa danlalacewar tarbiyya da zinace zinace da shaye shaye don neman biyan bukata.
Idan da Saudi da kuwait ko German ko ingila ko Dubai da sauransu sun rufe kasa suce baza su shigo da abinci daga wata kasa ba suga yadda za su kasance da talakawa, kowa ya sani kudin biredi da mai shugaban Sudan Albashir.ya kara sanadiyyar zamga zanga kenan saida ya bar mulki ya faru a kasashe da dama mun gani gwamnati da yawa sun rushe saboda tsadar rayuwa da karancin abinci.
Rashin kishi da tausayin talakawa da rashin imani ya kawo tsadar abinci da kayayyaki saboda an sa jari hujja masu hali.sun noma wasu sun saye abinci an barsu sai farashin da suka da suke sayarwa kanan Yan kasuwa masu neman.su sayar su sami abinci. An bar wasu shafaffu da mai sai abin da suka dama suke Yi. Masu tausaya wa su sayo su sayar su samu abinci mutane su samu rangwame duk an karya su, sun koma cikin talauci su day iyalansu da yaransu sun dukufa da addua Allah ya bi musu kadi shi yasa idan yau an toshe nan sai gobe can ta bude amma an kasa hankalta a nemi masana tattalin arziki da zantakewa da kasuwanci da malaman jamia da na addini a nemi shawarar su a dauka don a samu mafita saboda su shugabanni basa cikin wahala.
Idan gwamnati ta ga dama cikin kankanen lokaci farashi zai sauka a koma walwala kamar yadda suka samu kasar. Saboda ko abinci da kwastam suka kama aka rabawa maaikata a farashi mai.sauki ya watsu a cikin kasa dole farashin kayan masarufi ya sauka.
Ko yau idan kana da dan uwa kwastam idan ya ga dama zai iya maka dalilin sayen shinkafa da suka kama a dubu takwas buhu da manja da taliya da sauransu duk suna sayarwa masoyansu ko su tura musu kyauta a birni muna kallo.
Amma kada ku mance kayan masarufi na Yan kasuwa ne da suka sayo don su sayar su cida iyalansu aka kame harda motocin da ke dauke da irin wannan kaya duk Wanda yasan akwai ofishin kwastam a garin su ko daga bakin hanya ya leka zai hango kayan birjik suna ta lalacewa. Idan a Bauchi mutum yake yaje yalwa gidan kwastam daga kan kwalta zai hango kayan mutane da aka kama
A irin su Kano da Katsina da legas suna da manyan store da ake Kira ware house cike yake da kayan bayin Allah Yan kasuwa da aka kama Kuma an karya su da iyalansu da maaikatan su da Yan uwansu. A baya konawa ake Yi saida kumgiyoyin kare hakkin Dan adam suka tsaya kafin ake turawa Yan gudun hijra Wanda ya Dan lalace Kuma a kona. Wani lokaci har inda ake kona kayan masarufi talakawa ke bi su tone Wanda wutar bata Kai gare Shi ba su kwasa suje su ci.
Idan kaje mashigin ruwa a kudu da filayen jiragen sama da kan iyakoki sama da dubu wato bododin Nigeria duk zaka ga irin wannan kaya na Yan kasuwa da aka kama wanima Yana niger ko kamaru ko chadi ko cotona Yana ta.lalacewa an Hana a shigo da Shi Kuma dukiyar Yan kasuwa ne da za su amfani kasa a fita daga wahalar Amma saboda mugunta an musu jiki magayi an karya su.
Kada ku mance duk Wanda aka zalunta ba zai ce Allah ya Yi albarka ba saiko Allah ya tsine ko Allah ya Isa kuma Allah zai bi kadin sa.
Shi ya sa ko abinci suka ci baya maganin yunwa ko a sayarwa mutum kayan araha aci a gamu da lalura saboda kullum dan kasuwar da aka karya muguwar addua yakewa kasar da shugabannin wanima yasin zai sa ayi ta saukewa Allah ya bi masa kadi don haka kullum lamarin ke.kara lalacewa, talakawa kuka me mulki kuka jamiin tsaro kuka hatta dan banga kuka yake Yi.
Wanda baizo duniya bama Yana cikin uwarsa idan an mata scanning sai ace bshi da lafiya. Kai hatta jaririn da aka aifa uwa bata ci ba balle ya samu ruwan nono idan an gwada shi Sai ace yana da ulcer, wannan wane irin balaine a kasa me arzikin mai da noma da maadinai irin Nigeria.
Abin takaici karamin mudun shinkafa yar gida me tsakuwa naira 700 masara garinta 400 a nijer buhun shinkafa dubu 13 a Nigeria dubu 23 buhu. Kuma kowa ya sani mafi karancin albashi naira dubu 15 zuwa dubu 30. Me digiri a jaha albashi dubu 37 a federal dubu 60. Kurtun Dan sanda ko soja an bashi bindiga ya kwana a daji Yana tsaron kasa da jamaa albashinsa dubu 60 hakama ta yiwu ba a biya shi a kan lokaci ba idan ka je gidansa yana da iyali da Yan uwa dake gani yana aiki kullum suma masa waya abinci ya kare Kuma ace an samu nasarar yaki da cin hanci da rashawa. Ya kamata mu daina yaudarar kan.mu mu gayawa juna gaskiya a daina dorawa Allah laifi mu fito mu gayawa shugabanni gaskiya don su gyara.
Wallahi bana ganin laifin shugaban kasa Buhari saboda duk wahala da ake sha talakawa akwai Wanda basu yarda akwai matsala ta shugabanni bane cewa suke Allah ne. Alhali sai an gayawa shugabanni ana cikin wahala kafin su gyara don kada su gamu da boren talakawa tunda sun fi kowa.son zama a kujerar mulki cikin salama.
Amma tun da talaka yace ba laifin shugabanni bane talauci da tsadar abinci daga Allah ne to shi yasa Allah ya bar talaka da dabarar sa ya jira Allah ya masa ruwan kudi ko abinci daga sama shikenan, Amma a sani talakawa a arewa kirista da musulmi suna da hakuri da yiwa gwamnati uzuri saboda sun yarda da Allah. Amma Yan kudu ba za su ci gaba da zuba ido suna gani talauci da ganganci na musu cin kaca su zuba ido har Nan da shekara uku cikin wannan yanayi ba dole su fusata su kalubalanci gwamnati a kotu ko Kuma ta kowace hanya da suke ganin za su iya.
Ya kamata Yan arewa su lura Yan kudu sun koma.gefe sun Yi bakam sun Yi shiru hatta mataimakin shugaban kasa ya Yi shiru sun zuba mana ido don haka ya kamata mu hankalta mu nemi mafita a gyara kasa tun dare Bai yiwa Yan arewa ba.
Saboda duk da wahalar da ake sha wani lokaci da kudin ana neman abinci a saya babu. Abin takaici a jiya Ministan Noma Nanono ya fito a radio yana cewa baza su bari a shigo da abinci ba duk wahala da za a shiga saiko a shiga me yake nufi da wannan kalami ya nuna duk mutuwa da za a Yi saboda yunwa ayi bata dame su ba.
Nigeria ba Niger bane mutum milyan 200 ba wasa ba idan noma ake Ina taki Ina kudi ina kwanciyar hankali ko filin nomar. Wanda ke Lagos ko kalaba.da kudanci ina zai yi nomar. A arewa an kawo yanayin da kana gonar idan aka sace ka sai an sayar da gonar da gidanka ba a fansheka ba, to ance milyan daya zuwa goma a kauye Wanda gidan da gonar suka Kai wannan.kudi sai attajirin gaske.
Shawara a nan mu fadawa kan mu gaskiya Allah ya kawo mana mafita ya mana maganin duk me hannu a cikin wannan wahala da tsadar abinci ko shi wanene Allah ya mana maganinsu tunda a cikin su babu annabi ko sahabi ko tabii Allah ka gaggauta kawo mana karshen duk wani shugaban da bai damu da halin talauci da yunwa da kunci na rayuwa da rashin aikin Yi da ake fama da shi ba. Allah ka kawo mana mafita cikin gaggawa ba don halin.mu ko halin.wawayen cikin mu ba.
Ya Allah ka sani ko rantsuwa na Yi ba zanyi kaffara ba gidajen shugabanni ba a fiskantar barazanar yunwa ba a cin shinkafa yar gida. Allah ka bi mana kadi cikin gaggawa kasa su gane, idan ba masu ganewa bane Allah ka gaggauta kawo mafita ka mana maganinsu a ruwan sanyi don mu samu salama a rayuwa.
Daya Muazu Umar Hardawa Editor ALHERI newspapers Bauchi Nigeria 07011546797