AN RANTSAR DA SABBIN ALKALAN BABBAR KOTUN JIHAR KANO

0

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamna Kano Abdullahi Umar Ganduje OFR ya jagoranci rantsar da alkalai na babbar kotun jihar Kano wato Kano High Court, da ya gudana a fadar gwamnatin Kano.

Alkalan guda shida sun hada da :
1- Jamilu Shehu Sulaiman
2- Zuwaira Yusuf
3- Maryam Ahmad Sabo Mni
4- Sanusi Ado Maaji
5- Hafsat Yahaya Sani
6- Abubakar Abdu

An kuma nada babban sakatare guda daya wato Abba Aminu Bahaushe wanda aka tura shi maaikatar gidaje wato (Ministry of Housing).

Gwamna Ganduje ya taya su murnar wannan sabon matsayi da Allah Ya kai su, sannan kuma yayi kira a gare su da su ci gaba da bada gudunmawar su wajen ganin cewa sun ciyar da jihar su gaba da ma kasar su baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here