Malam Kabiru Makaho Na Shirin Dadin Kowa A Arewa24.

0

Cikakken sunanshi Rithwanullah amma an fi kiranshi da Mainasara amma a cikin shirin Dadin Kowa sunanshi Kabiru Makaho domin shi ne Script name nashi.

Haifaffen Haruwa ne da ke cikin Nassarawa da ke Karamar Hukumar Kankiya da ke Jihar Katsina. An haife shi a 1963 kuma bai taba zuwa makarantar Boko ba amma yayi karatun Allo a Zariya sannan ya rubuta littattafai akalla guda hudu. Biyu ba Turanchi, biyu ba Hausa.

Hot Dimond in Cold Blood, Cross Fire In Niger Delta, Gwagwarmayar Rayuwa, Inda Rabon Kura a Takobi. Su ne littattafan da ya rubuta duk da bai yi karatun Boko ba. Allah ya hore mashi nashi kwazon da hazaka ta bangaren rubuce rubuce.

Kwakwa, Shaawa da nacin kallon drama Ya taimaka mashi matuka wajen cimma wannan buri nashi na rayuwa duk da ya samu rangwamen gata wajen karatun Boko.

Ya fara harkar Drama Staging a Rex Cinema da ke Zaria inda suka kafa kungiya mai suna Zumunta Drama. Bayan wani lokaci lokaci sai Allah yayi mashi dawowa a garin Kano ya hadu da mutane irinsu Marigayi Katakore, Ibro a inda shi ne ya rubuta mafi yawancin drama na farko ba shi Ibro.

Bai yadda aka fara dora mashi Camera ba tun da farko don yin Drama ba Saboda rashin shaawar haka tun farko amma ya kware sosai wajen bada Ummurni watau Directing.

Daga cikin drama da ya bada Ummurni ko rubutawa sun hada da Bariki ba Gayya Bace, Sirki da sauransu.

Ya chanza raayinshi daga scripting ko directing zuwa fitowa a Drama ta Dadin Kowa sakamakon Jan raayinshi da wani abokinshi Muhammadu Tukur yayi ta hanyar janshi a karo na farko zuwa gidan Talabijin na Arewa 24 Kimanin shekaru Shidda da suka gabata.

Salisu Balarabe wani Bakatsine ya taimaka kwarai wajen Shawo kanshi na amsar goron gayyatar gidan Talabijin musamman kan shirin Garin Dadin Kowa.

A Eagle Access ne wajen da suka fara gudanar da harkar drama ta Garin Dadin Kowa. Garin ba Dadin Kowa yana nan a cikin Karamar Hukumar Doguwa da ke Jihar Kano. Ban da nan akwai garin a Gombe da Igabin Jihar Kaduna.

Daga cikin dalilin kafa shirin shi ne nuni a cikin nishadi ta hanyar haskaka ma mutane an Illolin yin bara, rashin zuwa makaranta musamman Yaya mata, nacin bara, rashin godiya Allah ya mabarata musamman makahi.

Ladingo matarshi ta cikin shirin wadda yake ma kirari da yar aljannah tana da matukar hakuri da jumriyar hitinashi. Amma ita kuma Bachogala akasin Ladingo ce. Daga cikin yayanshida yan jagoranshi akwai Kandala tana Karatu a School of Management Kano, Bintalo tana Secondary sai Alawiyya tana gidan Mijinta.

Ta bangaren Iyalinshi yana da Mata Daya da ya aura a ranar Asabar 15/9/1980, suna da yara Ukku amma daya ta rasu saura biyu daga ciki akwai mace daya da namiji daya da kuma jikoki.

Kabir Umar Saulawa
P. R. O
07034610481.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here